Saturday, April 19, 2025

Yadda ake saki da Sharuddan saki a musulunci


Yadda ake saki da Sharuddan saki a musulunci

Saki shine sauwake wa macen da kake aure Ku rabu da ita matukar lamarin zamantakewa yayi tsananin da daya daga cikinku zai kuntata da Yin illa ga juna

Allah Madaukakin sarki a cikin Alkur'ani mai girma ya na cewa: 
"Ya kai wannan Annabi (S.A.W) a duk lokacin da kuka yi nufin sakin mata,
to ku sake su cikin tsarkinsu (wanda mazajensu ba su kusance su ba a cikinsa) Kana ku lissafa (kwanakin) tsarkin, kuma ku ji tsoron Allah Ubangijinku, kada ku kuskura ku fitar da su daga gidajensu, kada su ma (matan) su kuskura su fita (a lokacin da suke cikin idda), sai dai idan har sun zo da alfasha mabayyaniya, to wadannan su ne iyakokin Allah".

Wanda duk ya ketare iyakokin Ubangiji, hakika ya zalunci kansa, (domin kuwa) ba ka sani ba ta yiwu Allah ya haifar da wani al'amari (na sulhu a tsakaninku)
bayan haka.

Bayani kan yadda hakikanin saki yake a musulunce:
Ta yiwu daya daga cikin dalilan da ya sa ake kiran wannan sura da
sunan surar saki (Talak) shi ne irin hukunce hukuncen sakin da
suke kunshe a cikinta makil, wanda wannan yana nuna mana irin
la'akarin da shari'ar musulunci ta yi dangane da al'amarin saki,
saboda irin hatsarin da yake da shi, domin abu ne wanda in har
ba'a yi da gaske ba, kuma ba'a yi shi yanda musuluci ya zo da shi
ba, sai ka samu ya taimaka wajen wargaza al'umma da tarbiyyar
iyali, da haifar da gaba da kiyayya a tsakanin dangi.

Kamar yadda rashin kiyaye hukuncin sakin ke iya haifar da aure
kan aure, wanda daga karshe a dinga haifan 'ya'ya marasa tabbas
din iyaye.
Kamar yadda kuma, shi saki ba wani abu ne wanda shari'a ke
karfafa gudanar da shi ba, bil hasali ma shi ne halas wanda Allah
ya fi ki, kamar yanda ya zo a mashahuriyar ruwaya daga Ma'asumi (S.A.W).

"Babu wani abu da Allah ya halatta kuma yake fushi da shi fiye da
saki.
Sai dai kuma wani abin tambaya a nan shi ne, mene ne yasa
shari'a ta halatta yin saki?
Amsa a nan ita ce a irin hali na zaman yau da gobe na ma'aurata a
wasu lokuta za ka samu cewa akwai wasu halaye wadanda suke
faruwa marasa dadi wanda in da za'a tilasta ci gaba da zama da
juna tare da wadannan halayen, to rayuwa zata yi ma daya daga cikin ma'auratan tsanani da kunci wanda zai iya kaiwa ga halaka da abin da ya yi kama da haka.

To saboda Allah ne mahaliccin kowa da komai, kuma masanin
abin da zai kai ya kawo, ya samar da magani da mafita a duk
lokacin da irin wadannan matsaloli suka bijiro a tsakanin ma'auratan, wanda wannan magani shi ne saki, duk da cewa ba'a son al'amarin ya kai ga haka, sai idan ya zama dole.

Me ake nufi da sakin mataye a cikin tsarkinsu:
Malaman tafsiri sun tafi a kan cewa ayar da ta zo a farkon wannan
sura tana bayani ne kan yadda ake saki, a inda take cewa idan har
an yi nufin saki, to a sake su a cikin tsarkinsu, abin da ake nufi da
haka shi ne, a sake su bayan sun yi wanka daga al'adarsu (haila)
kana mijin bai kusanci iyalinsa bayan wankan ba.

Wannan ma'anar ita ce wacce ta shahara gurin masana tafsiri, sai
dai akwai sabani tsakanin mazhabobi kan cewa wannan hukuncin da ayar nan ta zo da shi wajibi ne ta yadda idan mutum zai saki matarsa a tsarki da ya kusace ta a ciki ko kuma a halin tana haila
sai ya sake ta to shin ta saku ko ba ta saku ba?.
A nanne malamai suke da sabani ta yadda wasu suke ganin cewa,
a irin wannan halin sakin ya inganta wato hukuncin da ayar ta zo
da shi ba wajibi ba ne wasu kuma suke ganin cewa sam bai
inganta ba (ma'ana hukuncin da aya ta 20 ta zo da shi wajibi ne).

Ga kadan daga cikin ruwayoyin
Ma'ana:
Bukhari da Muslim sun ruwaito daga kutaiba daga lais bin sa'ad
daga Nafi'u daga Abdullah bin umar cewa: 
shi, Abdullah bin umar
ya saki matarsa saki daya a halin tana haila, sai manzon Allah
(S.A.W) ya yi umarni da ya mai da ita, kuma ya ci gaba da zama
da ita har ya zuwa lokacin da za ta yi tsarki ta sake yin wata hailar
a gidansa, kana yajira ta har sai ta yi tsarki daga wannan hailar
tata, to in ya so ya sake ta, sai ya sake ta yayin da take cikin
tsarkin da bai kusance ta a cikinsa ba, to wannan ita ce iddar da
Ubangiji Madaukakin sarki ya yi umarni da a saki mata a cikinta".

Ma'ana:
"Ya zo cikin sahih Muslim daga manzon Allah (S.A.W.A.) cewa:
A duk lokacin da wani mutum ya saki matarsa yayin da take cikin
al'adarta, lallai ya zama wajibi kada ya kula da wannan saki da ya
yi mata (ma'ana sakin bai yi ba) ya ci gaba da zama da matarsa
har zuwa lokacin da za ta yi tsarki, sannan ya sake ta idan ya ga
dama". Sahih muslim kitabut Talak juzu'i na2.

Ma'ana:
"An karbo daga Abu Ja'afar (A.S.) yana cewa: 
lallai sakin da Ubangiji Madaukakin sarki ya yi umami da shi a littafinsa kuma Ma'aiki (S.A.W.) ya sunnanta shi, shi ne mutum ya nisanci
matarsa, idan ta yi haila kuma ta yi tsarki, sai ya kafa mutum biyu
adilai a matsayin shaida kan cewa ya sake ta a halin tana cikin
tsarkin da bai kusance ta a cikinsa ba, sannan shi ya fi cancantar
ya mai da ita su ci gaba da zama, matukar ba ta kare idda ba
(tsarki ko jini uku), to don haka duk wani saki wanda ya saba ma
wannan Batacce ne, ba bakin komai yake ba, wato wanda aka yi
mata shi tana nan a matsayinta na matarsa".

To a nan muna fata mai karatu zai zabura wajen kokarin gane
hakikanin hukuncin da Allah da Ma'aikinsa suka bayyana ma
al'ummar musulmi dangane da saki a cikin idda wato a saki mace
tana cikin tsarkinta kamar yanda muke fatan mai karatu zai
kasance tare da mu har zuwa karshen wannan bahasin da kuma
wannan bayanin a inda zai ga dumbin hikimomi da suke kunshe a
cikin yin aiki da wannan umarni na saki a cikin tsarki.

Kamar yadda zai kara samun nitsuwa kan irin hukuncin da
Alkur'ani mai girma ya tabbatar, wanda da a ce al'ummar musulmi
za su yi aiki da shi, to hakika da an sami saukin yawan mutuwar
aure.
A ina ya wajaba mace ta yi idda:
Wani hukuncin da wannan ayar ke dauke da shi, mai muhimmancin
gaske, wanda dukkan malaman mazhabobin musulunci sun yi
ittifaki a kansa, shi ne, a duk lokacin da mutum ya saki matarsa,
saki na raja'i wato sakin da zai iya yin bikonta a cikinsa, to wajibi
ne ya bar ta, ta gama iddarta a cikin dakinta wato a cikin gidansa.

Bai halatta ya fitar da ita ba, kamar yadda yake ita ma bai
halatta ta fita daga gidan ba har sai ta gama iddarta, sai dai in ta
aikata alfasha, to a irin wannan hali ne kadai ake iya fitar da ita.
Kamar yadda ya wajaba ya ba ta matsuguni, haka nan kuma ya
wajaba ya ci gaba da ciyar da ita har zuwa lokacin da za ta gama
iddarta, domin kuwa matar da aka yi mata sakin da za a iya yin
bikonta, tana nan a matsayin mata.

Don haka ne ma bai halarta ya
auri kanwarta ko 'yarta, kamar yadda ba zai Kara aure ba, idan da
ma adadin matansa hudu ne, har sai ta gama idda.
Haka nan kuma akwai gado a tsakaninsu idan dayansu ya rasu a
halin iddar ba ta cika ba, kana wajibi ne ya tufatar da ita a lokacin
iddar kamar yadda yake yi a da, a takaice dai, tana nan a matsayin
matsarsa har sai ta gama idda.

Shi ya sa ma ba ya halatta ta fita
zuwa unguwa sai da izininsa, kamar dai yadda take a da kafin ya
furta sakinta.
Dangane da al'amarin da ya shafi mai da ita, shi ma abu ne wanda
dukkannin malamai sun tafi a kan ganin cewa mutum yana da ikon
da zai mai da matarsa wacce ya saka irin sakin da ake yin kome a
cikinsa (wato sakin da bai wuce daya ko biyu ba kana kuma aka yi
shi kamar yadda shari'a ta zo da shi) a duk lokacin da ya ga damar
mai da ita to yana da ikon yin haka, ba tare da neman izinin wani
ba, ko da kuwa ita kanta matar bata yarda ba matukar iddar ba ta kare
ba, to wuka da nama na hannun mijinta.

Amma da zai yi sakaci har
iddarta ta kare to bai da ikon da zai iya mai da ita sai ta yarda
sannan sai an daura sabon aure.
Kamar yadda an so, matar da aka yi wa sakin kome, ta dinga
yawan yin kwalliya don jawo hankalin mijinta, kamar yadda shi
ma, in ya so mai da ita zai iya yin hakan a aikace, wato ta hanyar
yi mata wani Alheri ko kyaututtuka.

Kamar yadda Ayar Alkur'ani ke cewa "Idan sun yi dab da karewar iddarsu to ku cigaba
da zama da su (bayan kun mai da su) ta kyakkyawar hanya, ko
kuma ku rabu da su ta kyakkyawar hanya, kana (a lokacin da za ku
yi sakin) ku tsai da shaidu biyu adilai daga cikinku,  (ku kuma
wadanda aka nemi ku yin shaidar) ku tsai da shaidar domin Allah,
to da wadannan (abubuwan da suka gabata ne) ake wa'azi da su
ga dukkannin wanda ya yi imani da Allah da ranar tashin Alkiyama
kuma duk wanda ya ji tsoron Allah Madaukakin Sarki zai sanya masa mafita.

To wannan shi ne irin hukuncin da Allah ya zo da shi a littafinsa
sai dai abin tambaya a nan musulmi na aiki da shi ko a'a?

Shin ana iya sakin mace saki uku lokaci guda?
Yana daga cikin hukunce-hukuncen da suka shafi saki na sunna,
wadanda aka sami sabani tsakanin malamai a cikinsu, a saki mace
saki uku lokaci guda, da kuma wajabcin kafa shaidu adalai a
lokacin da za'a yi saki.

A inda mafi yawan malaman ahlus sunna suka tafi a kan ingancin
aukuwar saki uku a lokaci guda, wato a yi wa mace saki uku cikin
lafazi daya tak kuma ta saku saki uku alhali da can ba wata igiyar
aure da ta katse a tsakaninsu.

Bisa dogaro da suka yi da wasu sashe na ruwayoyi da ke magana
kan saki duk da cewa ruwayoyin da suka zo a wannan babin sun
kasu kashi biyu, wasunsu suna nuna cewa, saki uku lokaci guda ya
inganta, wasunsu kuma na nuna cewa saki uku lokaci guda daidai
yake da saki daya, ko da kuwa a wurare daban daban ne aka furta
sakin.
Kamar yadda ruwayoyi da dama ingantattu suke nuna cewa daga
baya ne, bayan Manzo ya yi wafati ake lizimta wa wanda ya yi saki uku
lokaci guda da cewa sakin nasa ya tabbata saki uku, wato bai da
ikon yin kome har sai matar da aka saka ta yi idda, ta yi sabon
aure.
Kamar yadda muslim ya ruwaito a cikin kitabut Talak babin
Talakus salas.
A inda ya fitar da hadisai uku da lafuzza daban daban wadanda
suke dauke da cewa lallai bayan wafatin Ma'aiki (S.A.W.A.) ne aka
lizimta wa mutane yin riko da saki uku a lokaci guda.

Ga daya daga cikinsu:
Is'hak bin Ibrahim da Muhammad bin Rafi'i sun zantar da mu,
(amma lafazin na Ibnu Rafi'i ne) Is'hak ya ce: Ma'amar ya ba mu
labari.
Ibnu Rafi'i kuma ya ce Abdur Razzak ya zantar da mu) Ma'amar ya
ba mu labari daga Ibnu Tawus daga babansa, daga Ibnu Abbas:
cewa: 
Saki uku a lokacin Manzon Allah da Abu bakar (r.a.) da
shekaru biyu na halifancin Umar (r.a.) ya kasance ana lissafa shi a
saki daya tak, sai Umar bin Khattab (r.a.) ya ce: Hakika mutane
suna gaggawa cikin lamarin da suka ga suna da wata dama ta yin
kome a cikinsa, me zai hana mu zartar da shi a kansu? 
Sai kuwa ya zartar da shi a kansu." Wato abin da wannan hadisi ke nunawa shi
ne cewa, zamanin Ma'aiki da zamanin halifancin Abu bakar (r.a.)
kana da shekaru biyu na halifancin Umar (r.a.), sahabbai sun
kasance in sun furta saki uku a lokaci guda yana nan a matsayin
saki daya tak, sai ya ce ba komai ya sa suke haka ba, face damar
da suke da ita, na mai da matan da suka saka da irin wannan
lafazi.

Don haka sai ya yi burin cewa me zai hana ya lizimta musu saki
ukun in sun farta shi a lokaci guda, duk da cewa lokacin Manzo ba
haka nan hukuncin yake ba? Sai kuwa ya lizimta musu, aka wayi
gari an ci gaba da aiki da wannan hukunci, duk da cewa bako ne in
an kwatanta shi da hukuncin da sahabbai suke a kai, a zamanin
Manzo da zamanin halifancin Abu bakar.

Kamar yadda duk sakin da aka gudanar da shi ba tare da shaidu
adilai ba, to wannan saki bai inganta ba.
Yadda sakin Sunna yake:
Kamar yadda bayanai suka gabata cewa wannan sura, an rada
mata suna da surar saki ce sabili da tarin hukunce hukuncen saki
wadanda shari'a ta wajabta da suke a cikinta, mai karatu ya
karanta wasu daga irin wadannan hukunce hukunce, kamar wanda
ya shafi yin iddar matar da aka yi mata sakin kome a gidan mijinta,
da wajabcin ciyar da ita na tsawon lokacin da take cikin idda,
kamar yadda saki ba a cikin tsarki ba, bai inganta ba wato dole ne
sakin ya zamo ya auku ne cikin tsarki da ba a sadu da ita a
cikinsa ba haka nan ma mun karanta batun rashin ingancin sakin
da aka yi shi ba gaban shaidu guda biyu adalai ba, kana kuma ya
gabata magana kan cewa dukkannin sakin da aka yi shi da lafazin saki uku a lokaci guda, irin wannan saki ba a bakin komai yake ba face saki daya.

Don haka muke ganin ya kamata a nan mu kawo cikon wasu
sharudda wadanda idan har ba su tabbata ba, to saki babu yadda
za a yi ya inganta a wajen Allah da Ma'aiki (S.A.W). 
Yana daga cikin irin wadannan sharuddan cewa shi saki dole ne a yi furuci da shi wato
da a ce za'a yi shi a rubuce kadai ko kuma da ishara kadai ko hannunka
mai sanda ga mutumin da ba bebe ko kurma ba, to a shari'a dai
irin wadannan sakin bai inganta ba.

Kamar yadda mafi yawan malamai sun tafi a kan wajabcin furuci da
saki ya kasance da siga kebantacciya wacce take da yaren larabci wato ita ce fadin mai saki ga matarsa: (Anti talikun)
Wato "Anti talikun" Ma'ana "Ke sakakkiya ce" 
Sai dai kuma sun tafi kan cewa dukkan wanda ba zai iya kawo
wannan furucin da yaren larabci ba, to zai iya yi da yaren da zai
iya, kamar yadda mutumin da ya gaza yin furuci da saki, ko da
kuwa shi ba kurma ko bebe ba ne a sakamakon wata larura, to irin
wannan zai iya amfani da ishara ko rubutu gurin sakin matarsa
duk da cewa an fi son rubutu a irin wannan halin.

Wani daga sharuddan da saki ba ya inganta sai da shi, shi ne nufi
wato wanda zai yi sakin ya zama ya kudurta cewa wannan kalma
da yake furtawa ta saki yana nufin aiwatar da saki ne da ita, don
haka mutumin da ya saki matarsa a halin yana maye ko kuma ba
da niyyar yin saki ba, to sakin bai yi ba.

Kamar yadda wanda ya furta saki a sakamakon takura da dole da
aka yi masa, nan ma sakin daidai yake da sakin mahaukaci, wato
bai inganta.

Wadannan su ne wasu daga cikin muhimman sharuddan da sai
sun cika kafin saki ya inganta
Hikimomin da suke Kunshe cikin saki irin na Sunna:

Daya daga cikin abin da yake kawo tabarbarewan tarbiyya shi ne
yawan samun rabuwar aure a cikin al'umma, duk da cewa shari'ar
musulunci ta halatta yin saki a lokacin da cigaba da rayuwar aure
ta faskara ta yadda in har ba a rabu ba to dayansu ko dukkansu za
su fada cikin mawuyacin hali.

Sai dai za ka samu cewa
shari’a ta dauki matakin domin kare mutane daga afkawa cikin
hatsarin rabuwar aure ta hanyar sanya ka'idoji da iyakoki wadanda
idan musulmi suka yi aiki da su, zai yi wahala wani ya saki matarsa kuma ta saku.

Irin wadannan matakan wadanda shari'a ta yi amfani da su wurin
kare mutane daga hadarin rabuwar aure su ne ake kira da
hikimomin da suke kunshe a cikin saki irin na sunnah. 

Ga kadan daga
cikinsu:
Yana daga cikin irin wadannan hikimomi a wajabta wa mace zama
a gidan mijinta bayan kuma ya sake ta har zuwa lokacin da za ta
gama idda, muddun dai sakin ba ba'ini ba ne kamar yadda aka
wajabta wa namiji cigaba da rike ta a gidansa, da ciyar da ita da
shayar da ita da tufatar da ita har tsayin lokacin da ta gama idda.

Kamar yadda akwai ruwayoyin da suke dauke da bayanai kan
yadda ya kamata matar da aka saka (sakin kome), ta kasance
kullum cikin ado da kwalliya da sa turare da kyautata dabi'u wadanda za su jawo hankalin mijinta ya yi sanyi, ya kuma Karkato  hankalinsa zuwa gare ta.

Wata hikimar kuma ita ce maganar a saki mace a cikin tsarkin da
ba a kwanta da ita a cikinsa ba, ta yadda idan anyi saki a halin an
sadu da ita a cikin wannan tsarkin to sakin bai yi ba, wato dole ne
a jira sai ta yi tsarki daga al'adanta.

Wanda wannan jiran abu ne
wanda zai iya taimakawa wajen hucewar fushin mijinta, ka ga sun
dawo sun ci gaba da zaman lafiya a tsakaninsu.

Kuma yana daga cikin manya manyan hikimomin da ke hana saurin aukuwar rabuwar aure, maganar kafa shaidu biyu adalai, wadanda idan da za ayi saki babu su ko kuma babu daya daga cikinsu, to
wannan sakin sam bai yi ba a shari'ance. 
Wannan magana ta
shaidu biyu adalai ta magance mana matsalar sakin mata da
tsakar dare, kamar yadda ko da an samu shaidu biyu matsawar ba
su sifantu da sifa ta adalci ba ko kuma daya daga cikinsu ba adali
ba ne shi ma dai saki bai yi ba.

Kamar yadda kuma shari'a take kwadaitar da cewa ya kamata miji
ya yi wa matar da ya saka, saki na sunna, (ya yi mata) ihsani wato
ya kyautata mata kyautatawa su rabu cikin mutunci, wanda tasirin
yin haka yana da yawan gaske, kadan daga cikin irin wannan tasiri
shine yadda matar ba za ta kullace shi a ranta ba ta yadda idan
akwai haihuwa a tsakaninsu, gaba da kiyayya ba za su faru ba
sakamakon irin wannan rabuwa ta mutunci da suka yi.

Idan kuma har ba 'ya'ya to zumunci ba zai rushe tsakanin danginta
da dangin tsohon mijinta wanda suka rabu cikin mutunci ba.

A nan za mu so mu cike wannan binciken da wasu kalmomi na
nasiha ga ma'aurata. 
Akwai tarin hadisai daga Ma'aiki (S.A.W.)
wadanda ke yin horo ga miji da mata kan lizimtan tsabta da
nesantar kazanta da duk wani abu wanda zai haifar da kyamar
juna, kana da aikata dukkannin wani abu da zai jawo kauna da
soyayya tsakaninsu, shin ta hanyar magana ne ko mu'amala ta
hanyar ado ne ko kuma zuwa da abin dariya da nishadi a
tsakaninsu.

Wani abin takaici sai ka samu wasu maza suna yin nishadi a
tsakanin abokan hirarsu amma da zarar sun iso soron gidan da
iyalansu suke ciki take sai ka ga sun murtuke fuska, kuma sun
shiga kaurara murya wai su manya ne, alhali kuwa fiyayyen talikai,
shugaban Manzanni Annabi Muhammad (S.A.W.) ga abin da yake fadi kan yadda ya kamata mu'amala ta kasance tsakanin miji da mata.

Kuma ya azurta shi ta inda bai yi tsammani ba, lalle duk
wanda ya dogara ga Allah to shi (Allah) ya ishe shi, hakika Allah
mai isar da al'amarinsa ne, lallai Ubangiji ya sanya wa kowane abu
iyaka.
Kuma wadanda suka yanke kauna daga yin haila cikin matayenku
idan har kuka yi kokwanton (suna da ciki ko ba su da shi) to
iddarsu wata uku ce, haka nan kuma matan da ba sa yin haila (su
ma iddarsu wata uku ce), ma'abuta ciki kuma iddarsu ita ce haife
cikinsu kana, wanda duk yaji tsoron Allah, (Allah) zai saukaka
al'amarinsa.

Wadannan (hukunce hukuncen) umarnin Allah ne da ya saukar
zuwa gare ku, kuma duk wanda ya ji tsoron Allah, to Allah zai kankare masa munanan ayyukansa kuma ya girmama masa lada.

"Mafifici daga cikinku shi ne wanda ya fi kyautata wa iyalinsa kuma
ni na fi ku kyautata wa iyalina."

Kuma akwai ruwayoyi da ke nuna mana karara irin illar da ke
tattare da rashin yin tsabtar ma'aurata.

Kuma dangane da ciyar da wadanda aka saka Mawadaci lallai ya ciyar daga wadatar da yake da ita, duk wanda kuma aka kuntata
masa arzikinsa (wato talaka) to lallai shi ma ya ciyar daga abin da
Allah ya ba shi, Allah ba ya kallafa wa wani bawa face gwargwadon
ikon da ya ba shi, (domin) ba da dadewa ba Allah zai kawo sauki
bayan tsanani.

Akwai da yawa daga cikin birane da alkaryu wadan da mutanensu suka kangare wa umarnin Ubangijinsu da manzanninsa sai muka yi musu hisabi matsananci kuma muka yi musu azaba nan take .
Sannan suka dandani musifa, kuma karshen al'amarinsu ya
kasance tabewa.

A sakamakon sabawar da suka yi wa umarnin Ubangiji sai Allah ya
tanadar musu azaba mai tsanani, don haka ya ku masu
hankalin da kuka yi imani kuji tsoron Allah, domin hakika Ubangiji
ya saukar da abin da yake tunatarwa a gareku.

Ya aiko muku da Manzo, wanda yake karanta maku ayoyin Allah mabayyana don ya fitar da wadanda suka yi imani kana suka yi aiki na gari daga nau'oin duhu zuwa ga haske duk wanda ya yi imani
da Allah kana ya yi aiki na gari to Allah zai shigar da shi gidajen
Aljanna wadanda koramu ke gudana a karkashinsu, suna masu
dauwama a cikinsu har abada, hakika (duk wanda ya shiga cikin
Aljanna to) Allah ya kyautata masa arziki.

Allah shi ne wanda ya halicci sammai bakwai kana ya halicci kasa kwatankwacinsu (wanda kuma a ko da yaushe) umarninSa na sauka a tsakaninsu (sammai da kassai) don ku san cewa hakika
Ubangiji mai iko ne kan kowane abu kana ku san cewa lallai ilimin
Allah ya kewaye dukkan komai.

Allah kai mana Jagoranci a duk lammuranmu.

Article Translation in English Language.

Divorce is letting go of the woman you are married to and leaving her if the social situation is so severe that one of you will end up harming each other. Allah Almighty says in the Holy Qur'an: 
"O Prophet (S.A.W) every time you intend to release a woman, then release them in their purity (in which their husbands do not approach them). 
If you count (the days of) purity, and fear God your Lord, do not dare to take them out of their homes, neither should they (the women) dare to go out (when they are in the Eid), unless they come with a large number of visitors, then these are the limits of God". 
Whoever transgresses the limits of God, has indeed wronged himself, (because) you do not know that it is possible for God to create a matter (of reconciliation between you) later. 
Information on how a real divorce is in Islam: 
Perhaps one of the reasons why this chapter is called The name of the chapter of divorce (Talak) is a type of divorce sentence they are contained in it, which this shows us the consideration of Islamic law regarding the issue of divorce, because of the kind of danger it has, because it is something that I have to deal with it was not done seriously, and it was not done the way Muslims brought it If not, you will find it helps to destroy the society and the discipline family, and cause enmity and hatred among relatives.

SHARE THIS

Author:

Etiam at libero iaculis, mollis justo non, blandit augue. Vestibulum sit amet sodales est, a lacinia ex. Suspendisse vel enim sagittis, volutpat sem eget, condimentum sem.

0 comments: