Abu Ayyub al-Ansari (R.A) Ya kasance babban sahabi kuma makusancin Annabi Muhammad (S.A.W.) daga kabilar Banu Najjar.Cikakken sunansa shine, Khalid ibn Zayd ibn Kulayb (R.A.).
Ya kasance daya daga cikin Ansarawan Madina wadanda Suka yi Maraba da zuwan Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare Madina a lokacin da yayi hijira daga Makkah.
Kuma a Gidan Abu Ayyub al-Ansari (R.A) ne Manzon Allah (S.A.W) ya sauka a lokacin da ya Isa Madina Inda ya zauna kusan tsawon watanni bajwai Kafin a gama gina masallacinsa da gidanshi.
Hakika Ayyub al-Ansari (R.A) yayi murna kwarai da Manzon Allah (S.A.W) ya kasance ya sauka a gidanshi, burin da kowane ba ansare yayi fatan cimmawa Amma Manzon Allah (S.A.W) Yace 'umurni ne, sai Inda taguwarsa ta tsaya Nan ne zai zama masaukinsa'.
Abu Ayyub Al'ansari (R.A) ya hidimta wa ma'aiki (S.A.W) matuka saboda da kaunar da yake mashi Kuma ya kasance Mai farin ciki da zaman Manzon Allah (S.A.W) a gidanshi.
0 comments: