Sayyada sumayya ta kasance sahabiyar Manzon Allah (S.A.W) ta farko da tayi shahada a hannun kafiran makka a lokacin da ake azabtar da ita da mijinta, Yasir ibn amr bayan sun karbi musulunci.
Ita dai Sayyada sumayya ta kasance baiwace ga sahabin Manzon Allah (S.A.W) Abu Hudhayfa ibn al-Mughira Kafin ya musulunta daga baya.
Ya aurar da sumayya ga bawansa Yasir ibn amr, Inda Suka haifi Ammar ibn yasir.
Bayan Kira zuwa ga Musulunci da Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya yi ne Sai Yasir da sumayya da dansu Ammar suka musulta, lamarin da ya fusata abun gidansu Hudhayfa ibn al-Mughira Inda ya hada Kai da Abu jahl wajen azabtar da su da zafin rana da duka.
A sanadin wannan azabtarwan ne Abu jahl ya kashe sumayya da mashinsa Inda ta zama ta farko a Musulunci da ta yi shahada.
Shima yasir an kashe shi ta hanyar azabtarwan su Abu jahl, Al-mughira da sauran kafiran Makkah.
Shima Ammar ibn yasir sun azabtar da Shi Amma yaki yarda ya bar musulunci duk da tursasashi da Suka yi ya aibanta Annabi (S.A.W) Wanda ba da son ransa yayi ba.
Article Translation in English Language.
Sayyada Sumayya was the first companion of the Messenger of God (S.A.W) who was martyred by the Meccan infidels when she and her husband, Yasir ibn Amr, were being tortured after they accepted Islam.
Sayyada Sumayya was a slave to the companion of the Messenger of God (S.A.W) Abu Hudhayfa ibn al-Mughira before he converted to Islam later.
He married Sumaya to his servant Yasir ibn Amr, where they gave birth to Ammar ibn Yasir. And after the call to Islam by Prophet Muhammad, peace and blessings of God be upon him, Yasir, Sumayya and their son Ammar converted to Islam.
They were tortured by Al mughira, Abu jahl some Mecca infidels because of their conversion to Islam, and it was because of this torture that Abu Jahl killed Sumaiya with his spear and she became the first martyr in Islam.
Yasir was also killed by torture by Abu Jahl, Al-Mughira and other unbelievers of Makkah.
Ammar ibn Yasir also tortured him, but he refused to leave Islam despite the pressure they gave him, and he disobeyed the Prophet (S.A.W) who did it against his will.
0 comments: