Tarbiya ginshiki ne na cigaban kowace Al'ummar Kuma ana gina ta ne a kwakwalen mutane tun daga yarunta.
Duk Al'ummar da ta kasance bata da kyakkyawar tsari game da Tarbiya zata kasance koma baya a cigaba ta fuskoki da dama.
Domin sai da tarbiyane Al'umma ke Samun kowace irin cigaban rayuwa.
Saboda haka ya zama wajibi Al'umma mu kula da tarbiyar yaranmu tun daga farkon shekarunsu har zuwa lokacin da zasu iya fahimtar abun da yake daidai da Wanda ba daidai ba.
Tarbiyar Yara a musulunci tana farawa tun lokacin da yaro ya fara mu'amala da mutanen dake Kusa da shi, wajibin iyayene su tabbatar sun kula da yadda yaronsu ke mu'amala da juma'a musamman a shekarun farko na fara magana da fahimtar Mutane.
Iyaye sune abun koyi na farko ga kowane yaro, musamman mahaifiya wacce take tare da yaro a Koda yaushe.
Wajibin iyaye ne su kiyaye kalmomi ko zantukan da zasu rika amfani da shi lokacin da yaronsu ke tare da su, dole ne a guje munanan kalamai kamar na zagi ko aibantawa ko makamancin hakan domin shi yaro Yana kwaikwayon duk wani Abu ne da yaji ya fito daga bakin mahaifiya ko mahaifi....
Article Translation in English Language.
Education is the foundation of the development of every nation and it is built in the brains of people from their childhood.
Any community that does not have a good plan for education will be a setback in development in many ways.
Because it is only through education that the community achieves any kind of improvement in life.
Therefore, it is the duty of the community to take care of the education of our children from their early years until they can understand what is right and what is wrong.
Children's education in Islam starts from the moment a child begins to interact with the people around him, it is the duty of parents to ensure that they take care of how their child interacts with others, especially in the first years of speaking and understanding people.
Parents are the first role model for every child, especially the mother who is with the child all the time. It is the duty of parents to guard the words or expressions that they will use when their child is with them, they must avoid bad words such as insulting or insulting or the like because the child imitates everything that comes from the mouth of the mother or father....
0 comments: