Sunday, April 6, 2025

Son juna da girmama juna a musulunci

Son juna da girmama juna a musulunci

Musulunci ya koyar damu son juna da girmama juna, ko mun San juna ko bamu Sani ba, da Kuma kyautatawa juna zato, da fadin alkairin junanmu. 

Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi ya ce "Imanin dayanku baya cika har sai kaso ma dan uwanka abun da kake so ma kanka".

Haka zalika a cikin Wani hadisin Yana cewa "babu soyayya a tsakanin mutane biyu matukar kuskuren farko da daya daga cikin su yayi sanadin sabani a tsakaninsu". [Al adab Almufrad 401]
Ma'ana duk Musulmin ya kamata yaso Musulmi Dan uwansa ta hanyar yin masa uzuri a lamuransa da kyautata mashi zato.

Saboda haka 'yan uwana Musulmi mu zamo ma su kaskantar da kai da girmama juna, Kar muyi fariya ko dagawa. Mutukar muna bukatar samun daraja daga Ubangiji Allah Madaukakin sarki.

Mu tuna wasiyyar Bawan Allah Luqman (AS) da ‘Dan’sa Inda yake ce mashi
“Kuma kada ka rika dauke wa mutane fuskarka, (dan girman kai) kuma kada ka yi tafiya a cikin ƙasa kana takama da dagawa. Lalle ne, Allah bã Ya son duk wani mai takama mai fariya.” 
(Luqman 31:18)

Hakika duk wanda yayi riko da wadannan dabi'un, yayi riko da Alkairin da zai kara shi daraja Kuma ya kai shi zuwa AlJannah. 

Allah Ya tsaremu da Alfahari da dagawa. Amin.

Article Translation in English Language.

Islam teaches us to love each other and respect each other, whether we know each other or not, and to be kind to each other, and to say good things to each other. 

The Messenger of God, peace and blessings of God be upon him, Said, "None of you [truly] believes until he loves for his brother that which he loves for himself. [Al-Bukhari] [Muslim].." 

Similarly, in another hadith, the Beloved Prophet says "there is no love between two people in which the first mistake of one of them causes a conflict between them". [Al Adab Almufrad 401] 

This mean, every Muslim should love his fellow Muslim by apologizing to him in his affairs and being kind to him. 

Therefore, my Muslim brothers and sisters, we must humble ourselves and respect each other, do not be proud or arrogant. 
We all need to be honored by God Almighty. 

Let's remember the advice Servant of God Luqman (AS) to his son where he said to him 
"And don't show your face to people, (arrogance) and don't walk in the land boasting and boasting. Indeed, God does not like anyone who is proud and arrogant." Surah (Luqman 31:18) 
Indeed, whoever adheres to these values, adheres to Al-Qair that will increase his honor and take him to Jannah InshaAllah. 

May God protect us with pride and exaltation. Amen.

SHARE THIS

Author:

Etiam at libero iaculis, mollis justo non, blandit augue. Vestibulum sit amet sodales est, a lacinia ex. Suspendisse vel enim sagittis, volutpat sem eget, condimentum sem.

0 comments: