An ambaci Sunan Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi da Sunan MUHAMMAD sau hudu a cikin Alkur'ani mai girma.
An ambaci Sunan Manzon Allah (S.A.W) da Suna MUHAMMAD sau hudu a cikin Alkur'ani mai girma a cikin wadannan Surorin:
Suratul Al Imran aya ta 144, da suratul Al-Ahzab aya ta 40 da suratul Muhammad aya ta 2 da suratul Al-Fath aya ta 29.
Sannan Kuma an ambaci Sunan Manzon Allah (S.A.W) da Sunan shi Ahmadu sau daya a cikin suratul As-Saff aya ta 6, Inda Allah Madaukakin sarki ke cewa
"Kuma ku tuna Isa ɗan Maryama ya ce: "Ya Banĩ Isra'ila! Ni Manzon Allah ne zuwa gare ku, Mai gaskatawa ga Attaura (wanda ya zo) a gaba gare ni, kuma mai bayar da bushara da wani Manzo mai zuwa a bayana, sunansa Ahmad." To, a lokacin da ya je musu da hujjõji bayyanannu, suka ce: "Wannan sihiri ne bayyananne."
Yawancin sunayen da Allah (S.W.T) ke Kiran Manzon Allah (S.A.W) da su a cikin Alkur'ani na alkunya ne, Inda zaka ji Yace: Ya Hadi (Mai shiryarwa) ko Kuma Yace: Nazirun (Mai gargadi) ko ya kira shi da Nabi (Annabi) ko Rasul (Manzo) ko ya kira shi da Al Amin (Amintacce) da sauransu...
Hakika wannan zai tabbatar mana yadda Allah Madaukakin sarki ya ke girmama janibin Annabi (S.A.W), don haka Yan uwa yakamata mu ma kasance masu ganin Girman Annabi muhammad (S.A.W) da girmama janibinsa a cikin kowane irin hali.
Article Translation in English Language.
The Name of the Messenger of God, peace and blessings of God be upon him, and the Name of MUHAMMAD have been mentioned four times in the Holy Qur'an.
The Name of the Messenger of God (S.A.W) and the Name MUHAMMAD are mentioned four times in the Holy Qur'an in the following Surahs:
Suratul Al-Imran verse 144, Suratul Al-Ahzab verse 40, Suratul Muhammad verse 2 and Suratul Al-Fath verse 29.
And the name of the Messenger of God (S.A.W), Ahmadu is mentioned once in Suratul As-Saff verse 6, where God Almighty says
And remember, Jesus, the son of Mary, said: "O Children of Israel! I am the messenger of Allah (sent) to you, confirming the Law (which came) before me, and giving Glad Tidings of a Messenger to come after me, whose name shall be Ahmad." But when he came to them with Clear Signs, they said, "This is clear magic."
Most of the names that Allah (S.W.T) calls the Messenger of Allah (S.A.W) in the holy Qur'an are nicknames, where you will hear Him saying: Ya Hadi (The Guider) or He said: Nazirun (The Warner) or he called him Nabi (Prophet) or Rasul (Messenger) or He calls him Al Amin (Trustworthy) and so on...
Indeed, this will prove to us how the Almighty God respects the Prophet (S.A.W), so our brothers and sisters we should also see the Greatness of the Prophet Muhammad (S.A.W) and respect him in all situations.
0 comments: