Iddah ita ce zaman jira wanda Mata suke yi bayan sun rabu da mazajensu kafin su sake yin wani aure da wasu mazan.
Kuma iddah ta kasu kashi biyu ne. Akwai iddar rasuwa da kuma iddar rabuwa.
Iddar rasuwa ita ake kira takabah da hausa. Kuma ita dinma kala biyu ce. Akwai takabar mace ma ciki, Ita iddarta tana karewa ne daga lokacin da ta haihu.
Sannan akwai iddar mace wacce ba mai ciki ba, ita zata zauna ne na tsawon Watanni hudu da kwanaki goma.
Haka zalika Nau'in iddar rabuwa ta dalilin sakin mace ta kasu zuwa kashi uku ne kamar haka:
1. Iddar mace mai ciki.
2. Iddar mace mai jinin haila.
3. Iddar macen da bata fara jinin haila ba, ko kuma wacce ta fidda rai daga yin jinin haila (Tsohuwa).
Iddar mace mai ciki zata zauna ne har zuwa lokacin da ta haihu, Idan ta haihu to iddar ta ta kare. Koda kuwa a ranar da aka saketa din ne ta haihu.
Iddar mace mai haila, sai tayi jinin haila uku, Idan ta kammala jinin haila uku shikenan ta gama iddarta.
Iddar Tsohuwa ko kuma karamar yarinya mace wacce bata fara jinin haila ba, ita zata zauna ne har tsawon Watanni uku. Idan ta zauna tsawon wata uku to iddarta ta kammala.
Tsawon wannan lokacin mace zata zauna ne a gidan Mijinta tayi iddarta anan (Idan ba saki uku akayi mata ba).
Kuma Mijin nata ne zai kula da cinta da shanta da kayan adonta da dukkan dawainiyarta. Amma babu wata Mu'amalar aure da zai shiga tsakaninsu.
Mace Mai idda yakamata ta sani cewa a lokacin idda shari'a ba taba bayar da damar fita unguwa ko yawace-yawacen zuwa gidan biki ko gidajen kawaye ko kasuwanni ba. Sai dai abinda ya zama dole afita dominsa, kamar Zuwa asibiti, Ko gaida majinyaci (idan makusancinta ne).
Kuma ba zata rika kula wani Namiji wanda ba Muharraminta ba.
Don haka ba zata kulla maganar aure ba, kuma ba zatayi aure ba, har sai ta kammala iddarta.
Idan kuma takabah takeyi, to akwai karin wasu dokokin kamar rashin yin ado ko kwalliya, da sauransu.
Yakamata mace ta san cewa duk auren da aka kullashi kafin cikar iddah, to wannan auren bai dauru ba.
Wassalamu Alaikum.
Allah shine masani.
Article Translation in English Language.
Iddah is the period of waiting that women do after they divorce their husbands before remarrying with other men. And the iddah is divided into two parts.
There is the idda of death and the idda of separation. The death ceremony is called takabah in Hausa.
And it is also two colors. There is a widow who is pregnant, and her Idda is protected from the moment she gives birth.
And there is the Iddah of a woman who is not pregnant, she will stay for four months and ten days.
In the same way, the type of divorce due to the divorce of a woman is divided into three categories as follows:
1. Iddar of a pregnant woman.
2. Iddar of a menstruating woman. 3. Iddar of a woman who has not started menstruating, or who has given up on menstruating (old woman).
The iddar of a pregnant woman will remain until the time she gives birth. If she gives birth, her iddar will end.
However, she gave birth on the same day she was released. Iddar of a menstruating woman, she has three menstrual periods.
If she completes three periods, then she has completed her period Iddar Ghowa or a young girl who has not started menstruating, she will stay for three months.
If she stays for three months, then her Iddah is complete.
During this time, the woman will stay in her husband's house and do her Idda here (If she has not been divorced three times).
And her husband will take care of her, her drinking, her jewelry and all her duties.
But there is no marriage between them.
An idda woman should know that during the Eid, the law never allows her to go out of the neighborhood or to go to the party house, friends' houses or markets.
Except for what is necessary to go for it, such as going to the hospital, or greeting the patient (if it is close to her).
And she will not take care of a man who is not her Muharram. Therefore, she will not enter into marriage, and she will not marry, until she completes her Iddah.
And if she wears takabah, then there are other rules such as not to wear makeup, etc.
A woman should know that all marriages that were concluded before the completion of iddah, then this marriage is not binding.
0 comments: