Rashin yin magana ga da uwanka Musulmi (gaba) a Musulunci haramunne, domin Manzon Allah (S.A.W) ya ja hane mu da yin hakan.
Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace :
"Bai halatta ga musulmi ya kaurace ma dan uwansa Musulmi sama da kwanaki uku ba. Suna haduwa sai wannan ya dauke kansa, wannan ma ya dauke kansa, Amma mafi alkhairi acikinsu shine wanda ya fara yiwa dan uwansa sallama".
Imamu Malik da Bukhari da Muslim da Abu Dawud da Nisa'iy ne suka ruwaitoshi hadisin.
Acikin wata ruwayar ta Muslim da Nisa'iy kuma,
Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya kara da cewa wanda duk ya kaurace wa Dan uwansa Musulmi sama da kwanaki uku, idan ya mutu wuta zai shiga".
Kuma acikin wani hadisin ma Manzon Allah (S.A.W) yace
"A kowacce ranar Alhamis Ana gafarta ma kowanne musulmin da ba ya yin shirka. Sai dai mutane biyun da suke kiyayya (gaba) da juna, za'a ce wa Mala'iku "Ku dakata ma wadannan har sai sun shirya da junansu".
Don haka 'yan uwa Musulmi yakamata mu guji yin gaba da junanmu, mu kasance masu hakuri da yafiya ga wadanda Suka cuce mu ko Suka zalunce domin yin koyi da fiyayyen halitta ANNABI MUHAMMAD (S.A.W).
A matsayin Ka na Musulmi idan Ka fahimci wasu basa ma junansu magana, to kayi kokarin sulhuntasu domin samun lada a wajen Allah.
Allah Madaukakin sarki ya kare mu daga sharrin shaidan ya Kuma Kara hada kawunanmu domin cigaban addinin musulunci baki daya.
Article Translation in English Language.
Not talking to your Muslim brother is forbidden in Islam, because the Messenger of God (S.A.W) has forbidden us to do that.
The Messenger of God (peace be upon him) said:
"It is not permissible for a Muslim to stay away from his Muslim brother for more than three days.
When they meet, this one takes his head off, this one takes his head off, but the best among them is the one who greets his brother first".
The hadith was narrated by Imam Malik, Bukhari, Muslim, Abu Dawud and Nisa'i.
In another narration by Muslim and Nisa'i, The Messenger of God (peace be upon him) added that whoever abstains from his fellow Muslims for more than three days, when he dies, he will enter Hellfire.
And in another hadith, the Messenger of God (S.A.W) said "On every Thursday, every Muslim who does not commit shirk is forgiven,
Except for the two people who hate each other, it will be said to the angels, "Wait for these people until they are ready with each other".
Therefore, Muslim brothers and sisters, we should refrain from antagonizing each other, be patient and forgive those who have hurt us or wronged us in order to imitate the best of creation, PROPHET MUHAMMAD (S.A.W).
As a Muslim, if you understand that others do not speak to each other, then try to reconcile them in order to get a reward from God.
May Allah the Almighty protect us from the evil of the devil and unite our heads for the development of Islam as a whole.
0 comments: