Mu'amala da mutane ta fuska mai kyau a Musulunci abu ne dake da matukar muhimmamci ga Musulmi domin gina alaqa da zumunci Mai karfi.
Malamai da yawa Sun ja hankalin Musulmi game da yin mu'amala Mai kyau da kowane mabiya addinai, domin yin koyi da fiyayyen halitta Annabi MUHAMMAD (S.A.W).
Domin da kyawawan dabi'unsa da mu'amalarsa da kafiran Makkah ne yayi nasaran kafa Addinin musulunci a duniya ta yadda muma sakon ya iso izuwa gare mu.
Haka ne ma yasa ANNABI MUHAMMAD (S.A.W). a Wani hadisin sa Wanda Imam Tirmizhi ya ruwaita yake cewa, "Musulmin dake mu'amala da mutane Kuma ya jure cutarwansu ya fi wanda ba ya iya mu'amala da mutane Kuma ya kasa jure cutarwansu"
Ma'ana duk Musulmin da yayi hakuri ya zauna a cikin Al'umma tsakaninshi da Allah da nufin alkairi gare su Kuma ya jure masu zaginsa da aibatashi kamar yadda Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi ya yi hakuri da cutarwar kafiran makka, to yafi Musulmin da ya kasa yin mu'amala da mutane Kuma ya kasa jure cutarwansu na maganganun banza da gulmace-gulmace da zaginsa.
Domin da kyawawan mu'amala ne Wanda ba Musulmi ba zaiyi sha'awan shiga musulunci idan ya fahimci cewa lallai musulunci addini ne da duk Wanda ke cikinsa yakamata a same da hakuri da yafiya da jinkan juna.
Article Translation in English Language.
Dealing with people in a positive manner in Islam is very important for Muslims to build strong relationships and friendships.
Many scholars have drawn the attention of Muslims about having a good relationship with all followers of religion, in order to imitate the best of creation, Prophet MUHAMMAD (S.A.W).
It's Because of his good manners towards the infidels of Makkah, he succeeded in establishing the Islamic religion in the world so that the message of Islam reached us nowadays.
An this is also why PROPHET MUHAMMAD (S.A.W) In another hadith, which Imam Tirmizhi narrated, he said, "The Muslim who deals with people and tolerates their harm is better than the one who cannot deal with people and cannot tolerate their harm."
In other words, every Muslim who is patient and stays (live) in the Ummah with intention for them and tolerates those who abuse him just as the Messenger of God, peace and blessings of God be upon him, was patient with the harm of the unbelievers of Makkah, is better than a Muslim Who couldn't tolerate the harm of other Muslims.
Because it is by showing good manners, a non-Muslim will be interested in joining Islam if he understands that Islam is a religion that everyone who is part of it should be patient, forgiving and kind to each other.
0 comments: