Taimama ibadah ce da Ake Yin a matsayin alwala ko wanka janaba idan mutum ya Rasa ruwa ko Kuma Yana halin rashin lafiya ta yadda yin amfani da ruwa zai iya Kara mashi ciwon da yake fama da shi.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi ya koyar da mu yadda zamu yi Taimama a lokacin rayuwar SHI (S.A.W).
Bukhari da Muslim sun ruwaito hadisi Daga Ammar bin Yasir (RA) wata rana janaba ta same shi bai sami ruwan da zai yi wanka ba, ga lokacin sallah yayi, sai yayi birkida a kasa yayi sallah, yazo wajen Annabi saw yayi masa bayani, sai Manzon
Allah (SAW) yace : ''Inna ma yakfika an taf'ala haa ka za.''
Ma'ana :
''Ai ya isheka ka aikata haka kawai".
Sai ya bugi kasa da tafin hannayensa masu albarka, sannan ya hure kurar, ya shafi bayan kowane hannu da Dan uwansa, sannan kuma ya shafi fuskarsa da hannayensa.''
Haka Kuma Al-Haafiz ibn Hajar ya kawo wata ruwayar cewa:
''Ya dora hannayensa akan kasa, sannan ya kakkabe, ya shafi hannunsa na dama, da hannunsa na hagu, kuma ya shafi hannunsa na hagu da hannun na dama, sai ya shafi fuskarsa.''
Kuma har wa yau Ibni Hajar din ya kawo wata ruwayar a cikin
Fathul-bari, daga Ismail ya ruwaito shi a wannan lafazin:
''Ai hakan ya isheka, ka dora hannayenka akan kasa, sai ka huresu, sannan kuma ka shafi hannun damanka da hannu hagunka, kuma ka shafi hannun hagunka da
hannun damanka, sai ka shafi fuskarka.''
YADDA AKE TAIMAMA
shine zaka ce : BISMILLAHI tareda da kulla niyar yin taimama a zuciyarka, sai Ka bugi kasa sau daya da tafin hannunka a wuri mara laima mai tsabta ko dutse Mai tsafta, ka kakkabe hannayenka, sannan
ka shafi bayan hannunka na dama da tafin hannunka na hagu, sai ka shafi bayan tafin hannunka na hagu da tafin hannunka na dama, kuma zaka tsaya dai dai wuyan hannu, sai kuma ka shafi fuska da hannayenka sai kayi Addu'ar da ake yi bayan kammala Alwala, duk iri daya zakayi idan kagama taimama. Wato :
''Ash hadu Al Lailaha
illallahu wahdahu lasharikalahu, wa Ash hadu Anna Muhammadan abduhu warasuluhu.''
''Allaahumma aj'alni mina tawwabina waj'alni minal
mutadahhirina.''
Article Translation in English Language.
Taimama is an act of worship that is performed as an ablution or ghusl when a person loses water or is sick so that using water can increase the pain he is suffering from.
The Messenger of God, peace and blessings of God be upon him, taught us how to help during his (S.A.W) life.
0 comments: