YADDA AKE YIN SALLAR IDIN BABBAR SALLAH (EID UL KABIR) DA KARAMAR SALLAH (EID UL FITR).
Sallar idi sallah ce da Al'ummar Musulmi dake daukacin duniya ke gudanarwa a duk shekara a lokacin da aka kammala azumin watan Ramadan (karamar sallah ko kuma Eid Al FITR da larabci) da Kuma 10 ga watan Zul hijjah (babbar sallah ko Kuma Eid ul Kabir da larabci)
Ita Sallar idi babba ko Karama duka Sunna ce awajen dukkan Musulmi, idan Mutum ya Rasa su Bai Zama Dole Akansa Sai Ya Rama Ba.
* Amma Ya Halasta idan Mutum Ya Rasa Sallar Idi Acikin Jam'i da Yayi Shi Kadai, Ko Kuma Dashi Da Mutanen da suka Rasa Zasu Iya Yin Jam'i.
* Ba'ayin Nafila a masallacin idi, anaso ne Ka Zauna Kayi Wasu Ibadu ne Na Wuridi Ko Salati ga fiyayyen halita Annabi MUHAMMAD (S.A.W).
Yadda Ake yin sallar idi:
Niyyah:
* "Nawaitu Iqtida'a bil imami Salatal Idil Kabir Sunnatun Lillahi Billahi".
!
* Idan Kuwa Kai Kadai ne Ko Kuma Kaine Liman sai Kace: "Nawaitu Salatal idil Kabir Sunnatun Lillahi Billahi".
* Raka'ar Farko, Zakayi Kabbara Bakwai Har da Kabbaran Harama.
* Sai Ka karanta Suratul Fatiha Da Sura (Amma Anfi So Ka karanta Suratul Suratul A'ala).
* Raka'a Na biyu Zakayi Kabbara Shida Harda Kabbaran Mikewa.
* Sai Ka Biya Fatiha Da Sura {Amma Anfi So Ka Biya Suratush Shamsi}.
* A Tsakanin Kowacce Kabbara Anaso kayi Salati Ga Annabi Muhammadu S.A.W. Koda kuwa gajeruwace;
Masali: Allahumma Salli Ala Sayyidina Muhammadin Wasallim Ko Allahumm Sallai Ala Sayyyidina Muhammadin Haqqa Qadrihi Wa Miqdarihil Azim.
Amma Ba Sai Lallai Wadannan Salatan Ba, zaka iya yin kowane salati.
* Sannan Kuma ba'a Daga Hannu Wajen Wadancan Kabbarorin sai dai idan Kabbaran Harma ne.
*Wannan Sallar Mu yi Kokari Mu koyama Matan mu da 'Ya'yanmu Wadanda suke a gida basu sami daman zuwa Idi ba.
* Kada Ka Tafi Idi amma kabar matarka a gida bata Iya Ba.
*Allah Ka Taimakemu Kuma Kasa Mu yi Sallar Lafiya Albarkacin Annabi Muhammadu S.A.W.
Article Translation in English Language.
HOW TO PRAY FOR EID UL KABIR AND SMALL PRAYER (EID UL FITR).
The Eid prayer is a prayer that the Muslim community around the world conducts every year on the 1st day of Shawwal (Eid al-Fitr in Arabic), and on the 10th of Zul Hijjah (Eid ul Kabir in Arabic). It is the Sunnah for all Muslims to pray both Eid Al fitr and Eid ul Kabir.
* But it is permissible if a person misses the Eid prayer in a congregation that he performs alone, or if he is joined by people who missed it, they can perform the congregation.
* Nafila prayer in the Eid mosque is not allow, it's suggested to sit down and do some Azkar or Salawat to the best creature, Prophet MUHAMMAD (S.A.W).
0 comments: