Zakkar fidda Kai (Zakka Al fitr) zakka ce da ta zama wajibi ga Musulmin da yafi karfin Abin da zai ci na wunin ranar idi Inda zai fitar yaba Wanda bai dashi.
Zakkar fidda-kai wajiba ce akan dukkanin musulmi, yaro ko babba, mace ko namiji, cikakken ɗa ko bawa (matuƙar akwai halin yinta a lokacin).
Don haka wajibin fitar da zakkar fidda Kai ya rataya ne a wuyan Wanda ke ciyar da mutum, misali wadanda kake karkashin ciyarwanshi idan mutum bashi da halin biya, kamar bawa da kananun Yara ko iyalanka.
Tambayoyi da Amsa game da zakkar fidda Kai.
Me ake bayarwa a zakkar fidda-kai?
"Ana bayar da abinci ne sa'i ɗaya, malamai suka ce duk irin nau'in abincin da aka fi ta'ammuli dashi a wannan yankin, kamar shinkafa, masara, gero, da dai sauran su"
"Menene ma'aunin zakkar fidda-kai?"
"Abinda yake na umurni gameda ma'aunin zakkar fidda-kai, shine sa'i ɗaya na abincin garin, kuma awonsa shine kilo, kimanin kilo uku kenan"
Yaushe ne ake bayar da zakkar fidda-kai?
"Ana bayar da ita ne a ranar 28th, 29th, 30th, (na Ramadan) har izuwa daren idi, kuma ana iya bayar da ita a ranar idi kafin a tafi sallar idin".
Menene dalilin bayar da wannan zakkah?
"Domin a nuna godiyar Allah bisa ga ni'imarsa da jin daɗi ga bayi gameda sauke azumi da kuma cika shi".
Wanene ake bawa zakkar fidda-kai?
"Babu wanda ake baiwa face sai talaka"
Menene umurni gameda wakilta yaro ko wani gameda bayarda zakkah a lokacin da baka nan?
"Ya halatta mutum ya bada izini ga ƴa'ƴansa domin su fitar da zakkar a madadinsa akan lokaci koda kuwa shi baya ƙasar ma".
Shin ya halatta ga talaka ya nemi wani ya kawo masa zakkar fidda-kai?
"Eh ya halatta (ka nema a baka zakkar).
Akwai wani abin da ake faɗa ne na musamman a lokacin bayar da zakkar?
"Mu dai bamu san wata addu'a ba ta musamman da ake yi a lokacin bayar da zakkar fidda-kai".
Shin ya halatta a fitar da (a bayarda) zakkar fidda-kai da kuɗi?
"Bai halatta a fitar da zakkar fidda-kai da kuɗi, abisa fahimtar malamai da yawa, sabida ya saɓawa tsarin Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama da sahabbansa".
A ina zaka bayarda zakkar fidda-kai?
-
"Zaka bayarda zakkar fidda-kai ne a ƙasar da kake cikinta a lokacin buɗa baki, (lokacin kammala azumi), koda kuwa kana nesa ne daga asalin ƙasar ka"
Shin ya halatta a bada zakkar fidda-kai ga wanda ba musulmi ba?
"Bai halatta a bayarda zakkar fidda-kai ga kowa face sai daga talakawan musulmi".
Shin mutum zai iya karɓar zakkar fidda-kai kuma ya sayar da ita?"
-
"Idan wanda ya karɓi zakkar ya cancanta da ita, to ya halatta a gareshi ya sayar da ita da zarar ya karɓeta, (musamman idan yana da uzrin da yafi na abincin)"
Jinkirin bayar da zakkar fidda-kai har aka dawo daga sallar idi ba tareda uzri ba?
"Yin jinkirin bayar da ita har izuwa bayan dawowa daga sallar idi, wannan haramun ne, (bai halatta ba) kuma bata cika ba".
Article Translation in English Language.
Zakka Al fitr is a form of alms-giving which Islam considers required of every able[verification needed] Muslim at the end of Ramadan.
The purpose of Zakat al-Fitr is to enable poor people to celebrate Eid al-Fitr, the festival to break the fast of Ramadan.
In Islam it is mandatory from sunset on the last day of fasting and remains so until the beginning of Eid prayer (i.e., shortly after sunrise on the following day). However, it can be paid prior to this period. Some of the Sahabah (companions of Muhammad) paid it a couple days before Eid al-Fitr.
The amount of Zakat is the same for everyone regardless of their income:
the minimum amount is one sa` (four double handfuls) of food, grain or dried fruit for each member of the family, or an equivalent amount of money.
0 comments: