Cikakken Tarihin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (S.A.W)
Manzo Muhammad Al-Habib ɗan Abdullahi (Sallallahu alaihi wa sallam).
Muhammad ɗan Abdullahi ɗan Abdul-Muɗallibi ɗan Hashimi ɗan Abdu-Manafi ɗan qusayyi ɗan Kilabi, Sallallahu alaihi wa aalihi wa sallam,
(Harshen Larabci: Abūl-Qāsim
Muḥammad ibn AbdAllāh ibn Abd al-Muṭṭalib ibn Hāshim ibn Abd Manāf ibn Qusayy ibn Kilāb) nasabarsa maɗaukakiya tana tuqewa zuwa ga Annabi Ibrahim, alaihi salatu wassalam.
Mahaifiyarsa: Ita ce Aminatu (Aminah) ‘yar Wahbi ɗan Abdul-Manaf ɗan Zuhrata ɗan Kilabi (Radhi yAllahu anhuma).
Alkunyarsa: Abul-Qasim, Abu Ibrahim.
Laqabinsa: Almusɗafa yana da sunaye da suka zo a cikin Kur’ani mai girma kamar, Khataman nabiyyin, da Al’ummi da Almuzzammil da Almuddassir da Annazir da Almubin da Alkarim da Annur da Anni’ima da Arrahma da Al’abdu da Arra’uf da Arrahim da Asshahid da Almubasshir da Annazir da Ad’da’i da sauransu.
Tarihin haihuwarsa: 17 Rabi’ul Auwal Shekarar Giwa (571m) bisa mash’hurin zance gun Ahlul Baiti (a.s), an ce, 12 ga watan da aka ambata.
Wurin haihuwarsa: Makka.
Aikoshi: An aiko shi a Makka 27 Rajab yana ɗan shekara arba’in.
Koyarwarsa: ya zo da daidaito tsakanin dukkan halitta da ‘yan’uwantaka da rangwame na gaba ɗaya ga wanda ya shiga musulunci, sa’annan ya kafa shari’a maɗaukakiya da dokoki na adalci da ya karɓo daga wajan Allah (swt) su kuma musulmi suka karɓa daga gare shi.
Mu’ujizozinsa: Mu’ujizarsa maɗauwamiya ita ce Kur’ani amma waɗanda suka faru a farkon Musulunci suna da yawa ba sa kuma kirguwa.
Kiransa: Ya kira mutane zuwa ga Tauhidi a Makka a ɓoye shekara uku ya kuma kira su a bayyane shekara goma.
Hijirarsa: ya yi hijira daga Makka zuwa Madina a farkon watan Rabi’ul Auwal bayan shekara 13 daga aikensa, wannan ya faru ne sakamakon cutarwa daga kafirai gare shi da kuma ga sahabbansa.
Article translation in English Language
Complete History of Prophet Muhammad (S.A.W) Messenger Muhammad Al-Habib son of Abdullah (peace be upon him).
Muhammad son of Abdullah son of Abdul-Mudallibi son of Hashimi son of Abdu-Manafi son of Qusayyi son of Kilabi, Sallallahu alaihi wa aalihi wa sallam, (Arabic language:
Abūl-Qāsim Muḥammad ibn AbdAllāh ibn Abd al-Muṭṭalib ibn Hāshim ibn Abd Manāf ibn Qusayy ibn Kilāb) whose great lineage is leading to Prophet Ibrahim, peace be upon him.
His mother:
She is Aminatu (Aminah) daughter of Wahbi son of Abdul-Manaf son of Zuhrata son of Kilabi (Radhi yAllahu anhuma).
His Nickname: Abul-Qasim, Abu Ibrahim.
His nickname: Almusdafa has names that appear in the Holy Qur'an such as, Khataman Nabiyin, Al'ummi, Almuzzammil, Almuddassir, Annazir, Almubin, Alkarim, Annur, Anni'ima, Arrahma, Al'abdu, Arra'uf, Arrahim, Asshahid, Almubasshir, Annazir, Ad'di and others. History of his birth: 17 Rabi'ul Auwal Year of the Elephant (571m) according to the famous saying of Ahlul Bayti (a.s), it is said, 12th of the mentioned month.
His place of birth: Mecca.
He was sent to Makkah on 27 Rajab when he was forty years old.
His teaching: he brought equality between all creation and brotherhood and general concessions to those who entered Islam, and then he established the supreme law and the laws of justice that he received from God (swt) and the Muslims received from him. His miracles:
His eternal miracle is the Qur'an, but those that happened at the beginning of Islam are too many to count.
His call: He called people to Tawheed in Makkah secretly for three years and called them openly for ten years.
Download and Install this App (18MB)
Install from Google Play
Category | Lifestyle App |
Developer | Afri-Florecer |
Last Update | 10 March, 2025 |
Version Requirement | Minimum 4.4+ |
Application Version | 10.1 |
Application Size | 18MB |
0 comments: