Friday, March 28, 2025

Kabbarar da ake yi ranar sallar idi Karama (Eid Al fitr) da babbar sallah (Eid ul Kabir)

Kabbarar da ake yi ranar sallar idi Karama (Eid Al fitr) da babbar sallah (Eid ul Kabir)

Sallar idi guda biyu a shekara, sallar idi Karamar sallah wacce Ake kira Eid Al fitr da Kuma idi sallah babba wacce ake kira Eid ul Kabir da larabci.

Sallar Idi sunna ce mai karfi ga duk wanda sallar Juma'a ya zamo wajibi a gareshi, Kuma mustahabbi ga wanda sallar Jumu'a bai zamo wajibi a kanshi ba, kamar mace da matafiyi da bawa. 

Lokacin Yin Salllar Idi

Lokacin sallar Idi tana farawa ne daga bayan hudowar rana har zuwa lokacin zawali wato lokacin Sallar Azahar. 

Sallar Idi raka'a biyu ce ba tare da wazana ko Iqama ba, kuma sharadi ne a yita a filin Idi ba a masallaci ba, sai dai Masallacin harami ko kuma garin da basu da Masallacin Idi suma za su iya yi a masallacin gari. 

Sallan Idi raka'a biyu a ke yi, a raka'an farko Liman zai yi kabbaran harma sannan yayi kabbara shida bayan kabbaran harma sai ya zamo kabbara bakwai (7) ke nan, bayan kowace kabbara ana so Liman ya dan yi jinkiri kadan gwargwodon yanda mamu za su yi kabbara.

Bayan nan sai ya karanta Fatiha da Sura ya karkare raka'an, a raka'a na biyu kabbara biyar zai yi bayan kabbaran dagowa daga sujjada sai ya zamo kabbara shida (6) ke nan, ba'a so mutum ya daga hannu yayin kowani kabbara sai dai kabbaran harma ita kadai, wanda ya zo masallacin Idi ya samu Liman ya riga ya gama kabbarori har ya soma karatu, sai yayi kabbaran harma sannan yayi kabbarori shida sannan ya ci gaba da koyi da Liman.

Idan kuma ya zo ya samu Liman ya riga yayi wasu kabbarori sai ya shiga sallan ya ci gaba da kabbara tare da Liman idan Liman ya gama kabbaranshi ya fara karatu, sai ya biya kabbarorin da suka yi masa fauti. 

An so idan kuma mutum bai samu sallan Idi ba yayi shi kadai a masallacin Idi ko a Masallacin gari. Imamu Malik ya ce makaruhi ne mutum yayi wata sallan nafila gabanin sallan Idi ko bayana Sallan Idi a Masallacin Idi, sai dai wadanda suke yi a Masallaci su wadannan bai zamo makaruhi a wajensu suyi wata nafila gabanin Idi ko banyan Idi ba.


ABUBUWAN DA AKE  SO MUTUM YA AIKATA RANAR IDI

Abu na farko da ake so mutum yayi a ranar Idi bayan hudowan Alfijir shine wanka, sannan ya yi ado da sabon tufafi idan yana da shi, ko kuma tufa mai kyau, ya fesa turarai, an so ya taka da kafarsa zuwa Masallacin Idi yana tafiya yana yin kabbara haka ma an so idan ya zo masallaci yana jiran a tada salla ya ci gaba da kabbaran har sai an tada sallan, anaso mutum idan zai dawo gida ya bi wani hanyan daban ba wanda ya zo ta ita ba. 
Idan karamar salla ne anfi so mutum ya ci abinci kamin ya fita, idan ko a babban sallah ne anso kar ya ci komai ya bari sai ya dawo daga Idi yayi bude baki da naman layyansa. 

An so mutum ya karanta wadannan kabbarorin a lokacin tafiyarsa masallacin idi da lokacin da yake zaman jiran liman da lokacin dawowa.

Allahu Akbar, Allahu Akbar, La ilaha illa Allah, Allahu Akbar, Allahu Akbar wa Lillahil hamd


*Sunnar Yin Kabbarori Bayan Salloli Biyar Na Kwanukan Babban Sallah

An sunnanta yin kabbara a Babban Salla bayan kowani sallan Farilla a cikin kwanakin zaman muna, za'a fara kabbara daga bayan sallan Azahar na ranar Idi har zuwa sallan Asubahi na rana na hudu bayan ranar Idi. lafazin kabbaran shine:

ألله أكبر ألله أكبر لاإله إلاالله والله أكبر الله أكبر ولله الحمد،

(Allahu Akbar, Allahu Akbar, La ilaha illa Allah, Wallahu Akbar, Allahu Akbar wa Lillahil hamd).

EID UL KABIR and Eid Al fitr Takbeer




Yanda Ake Yin Kabbaran Shine:
----------------------------------------------------- 
Idan liman ya idar da sallan farilla zai yi kabbara da dan murya kadan wanda zai jiyar da Kansa da wanda ya ke bayansa sannan sauran jama'an da suka halarto masallaci suma su yi kabbara da kabbaran liman amma an ce kowa zai yi kabbaran shi ne shi kadai, ba za su hada murya daya ba.

Malamai sun tafi a kan cewa mutum zai yi wannan kabbaran ne a sallan Jam'i da sallan mai salla shi kadai, amma Imamu Shafi'i da Ahmadu bn Hanbal sunce wanda yayi Salla shi kadai ba zai yi wannan kabbaran ba.


Article Translation in English Language.

There are two Eid prayers in a year for Muslims, Eid Al-Fitr and Eid ul-kabeer. 

The Eid prayer is a strong Sunnah for anyone who is obligated to perform the Friday prayer, and it is recommended for the person who is not obligated to perform the Friday prayer, such as a woman, a traveler, and a servant.

SHARE THIS

Author:

Etiam at libero iaculis, mollis justo non, blandit augue. Vestibulum sit amet sodales est, a lacinia ex. Suspendisse vel enim sagittis, volutpat sem eget, condimentum sem.

0 comments: