Musulunci ya umurci dukkan Musulmi da kiyaye hakkin maƙwabcinsa ta hanyar kiyaye dukkan Wani abu da zai cutar da shi da Kuma yin abun da zai amfanar da shi.
Hakika abun takaici ne kwarai idan muka dubi yadda Al'ummar Musulmi da dama ba sa kulawa da hakkokin da Musulunci ya shimfida game da hakkin makwabtaka da irin yadda ya tsara wa ko wanne makwabci ya zauna da makwabcinsa lafiya, ta yadda zai girmama shi da kuma yadda zai gujewa cutar da shi.
Yana da kyau kowane Musulmi ya san hakkokin makwabcinsa da suke kansa, tare da sanin hanyoyin zama da shi, idan ya san hakan, shi zai sa ya zauna da makwabtansa kamar yadda addini ya tsara.
Ubangiji mai girma da daukaka ya fadi cikin littafinsa mai girma (Al kurani), cikin suratul Nisa'i aya ta 36 cewa:
"GAME Da IYAYE A KYAUTATA MASU, DA MAKUSANTA, DA MARAYU, DA MABUKATA, DA MAKWABCI NA KUSA".
Haka zalika Manzon Allah (S.A.W) ya;
"JIBRILU BAI GUSHE
BA YANA YI MIN WASIYYA GAME DA MAKWABCI HAR SAI DA NA ZACI CEWA ZAI GAJE NI"
(Bukhari da Muslim).
A Wani hadin Manzon Allah (S.A.W) Ya ce:
"WANDA DUK YA KASANCE YA YI IMANI DA ALLAH DA RANAR LAHIRA TO YA GIRMAMA MAKWABCINSA". (Bukhari da Muslim).
Saboda haka Idan muka yi duba ga wannan Aya dake suratul Nisa'i da wadannan Hadisai za mu fahimci girman kyautata wa makwabci da girmama shi, domin girmama shi ma yana nuna cewa
mutum ya yi Imani da Allah da ranar Lahira, rashin girmamashi Kuma Akasin haka.
WANENE MAKWABCI?
Malamai sun bayyana cewa makwabci shine wanda idan ka kirga gidaje arba'in daga jikin gidanka hagu da dama, gaba da baya dukkanninsu maƙwabtanka ne.
RABE-RABEN MAKWABTA DA HAKKOKIN SU A MUSULUNCI.
A tsarin Musulunci makwabta sun kasu zuwa kashi uku, kowanne da irin hakkokin da ke kansa, akwai mai hakki daya da mai hakkoki biyu da kuma mai hakkoki uku.
1.Makwabci Musulmi, makusanci (Dan'uwa): Shi wannan yana da hakkoki uku, hakkin Musulunci ga hakkin makwabtaka, ga kuma hakkin 'yanuwantaka*
2. Makwabci Musulmi: shi wannan yana da hakkoki biyu ne kawai, wato hakkin makwabtaka, sai kuma hakkin Musulunci*
3. Makwabci wanda ba musulmi ba: shi ma nan yana da hakki daya ne kawai wato hakkin makwabtaka.
Akwai hakkokin makwabtaka da dama, amma za mu dauko wasu daga ciki mu yi bayaninsu.
KAYUTATA WA MAƘWABCI:
Yana daga cikin hakkokin makwabtaka a kyautata masa ta kowanne hali, kamar aika masa da abin da ka dafa, bashi shawarwari da za su amfane shi, a kansa ko iyalansa, ko 'ya'yansa, tsawatarwa 'ya'yansa a kan abin da aka ga zai cuce su, domin kyautata wa makwabci yana kai mutum zuwa Aljanna.
Wani mutum ya je wajen Manzon Allah_Sallallahu_Alaihi wasallam ya ce:
"Ya Ma'aikin Allah shiryar da ni a bisa wani aiki, idan na tabbata a kansa zan shiga Aljanna, sai ya ce: "Ya Ma'aikin Allah ta ya ya zan san ni mai kyautatawa ne?
=Sai ya ce: Tambayi makwabtanka idan suka ce kai mai kayutatawa ne to shi ne, amma idan suka ce kai ba mai kayuatatawa ba ne, to ba shi ba ne".
Wannan Hadisi yana nuna mana cewa idan mutum yana son ya san matsayinsa, to ya tambayi makotansa sune shaidarsa a kan shi mai kyautatawa ne ko a'a.
Don haka wajibi ne mu zamo masu kyautata musu don mu samu kyakkyawar shaidar cewa mu masu kyautatawa ne, don in muka zamo masu kyautatawa, to mun kama hanyar zuwa Aljanna.
Ibn Umar ya kasance yana da makwabci Bayahude, idan ya yanka akuya sai ya ce: ku kai wa makwabcina Bayahude wannan
(Abu Dawud da Tirmizi).
Har ila yau, kiyaye mutuncinsa(Makwabci) da na iyalinsa da dukiyarsa suna daga cikin kyautatawa, domin Annabi Alaihissalam ya ce:
"Mutum ya yi zina da mataye goma shi ya fi sauki a gare shi da yin zina da matar makwabcinsa, mutum ya yi sata a gidaje goma shi ya fi sauki a gare shi da ya yi sata a gidan makwabcinsa" (Ahmad).
Ya zo cikin sunani Abu Dawud daga Aba Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce:
"wani mutum ya zo wajen Ma'aikin Allah ya kawo karar makwabcinsa, sai ya ce da shi, ka je ka yi hakuri, sai ya sake zuwa na biyu ko na uku, sai Manzon Allah ya ce:
jeka ka debo kayanka ka zuba a kan hanya, sai yaje ya sanya duk lokacin da mutane suka zo wucewa sai suka tambaye shi bisa halin da ya ke ciki, sai ya basu labarin irin cutar da makwabcinsa yake yi masa
Sai suka rinka la'antar makwabcin, sai makwabcin ya zo gare shi ya ce: ya dan uwana mayar da kayanka gidanka ba za ka kara ganin wani abu na rashin kyautatawa ba daga
gare ni har abada".
0 comments: