Azumin shittu Shawwal Azumi ne guda shida (6) da ake yi a watan Shawwal bayan kammala azumin watan Ramadan domin samun lada da tarin falala kamar yadda yazo a cikin hadisin Manzon Allah (S.A.W)
Imamu Muslim ya ruwaito da Hadisi ingantacce Daga Abu Ayyub Al'ansari (R.T.A) daga ANNABI (S.A.W) Ya ce:
"Duk Wanda ya Azumci Ramadan Sannan Ya bishi da Azumi shida (6) a cikin Shawwal ya kasance kamar wanda ya Azumci shekara".
Azumin kwana shida na watan sallah wato watan shawwal, Mustahabbi ne, wannan shine zancen mafiya yawa daga cikin malamai, wasu kuma suka ce makaruhi ne saboda jin tsoron kada a dauka cewa shima wajibi ne kamar na Ramadan.
Yadda Ake Azumtansa Malamai sunyi zantuka kamar haka:
1. Yin Azumin guda shida ajare a farkon watan.
2. Yin Azumin ajere ko a rarrabe duka daya ne a ko wani lokaci a cikin wata.
FA'IDAN AZUMIN SHAWWAL
1. Yin Azumi Shida (6) na Shawwal yana Cika ladan Azumin shekara.
2. Azumin Shawwal kamar Sallolin Nafiloli ne da'ake yi kafin
da bayan Sallaolin farilla. Wanda suke cika nak'asa da ta samesu
Allah ya Bamu Ikon Yin Azumin SITTU SHAWWAL don Albarkan ANNABI (S.A.W).
Article Translation in English Language.
Shittu Shawwal Fasting is six (6) fasts that are done in the month of Shawwal after the end of the fasting month of Ramadan in order to get rewards and blessings as mentioned in the hadith of the Messenger of God (S.A.W).
Imam Muslim narrated an authentic Hadith from Abu Ayyub Al-Ansari (R.T.A) from the Prophet (S.A.W) said:
"Whoever fasts Ramadan then follows it with fasting Six (6) in Shawwal is like someone who fasts a year".
Fasting for six days in the month of Shawwal, which is the month of Shawwal, is mustahabbi, this is the opinion of most of the scholars, and some say that it is makaruhi because they are afraid that it will be considered that it is also obligatory like Ramadan.
0 comments: