Monday, December 23, 2024

yadda ake yin sallar gawa

yadda ake yin sallar gawa

Sallar Gawa Ko kuma sallar janaiza Sallah ce da akeyi wa mamaci a lokacin da ya rasu kafin akaishi kabari Bayan anyi masa wanka an Sanya mashi likafani. Dukkanin Malamai na Mazhabobi sunyi ittifaqi akan cewa SALLAR GAWA (JANAZAH) FARILLAH CE TA KIFAYAH. (wato irin farillar nan wacce wani zai iya dauke ma wani).

Sai dai an ruwaito daga Asbag (daya daga almajiran Imamu Malik) cewar Shi Sunnah ce awajensa.

Za'a iya yin Sallar gawa akowanne Lokaci ko dare ko rana, Inji IMAM SHAFI'IY (RAH).

Amma IMAMU AHMAD DA IMAM ABU HANEEFAH (RAH) Sunce Makruhi ne ayi sallar Janazah alokutan nan guda Uku.


1. bayan Sallar asubah har zuwa fitowar rana.

2. Bayan sallar la'asar har zuwa faduwar rana..

3. Lokacin da Limamin Jumu'a ya hau kan mimbari yake khudubah.

Shi kuwa IMAMU MALIK (RAH) Yace za'a iya yin Sallar Janazah akowanne lokaci in banda lokacin fitowar rana da kuma lokacin faduwarta, yace Makruhi ne.


SHARUDANTA: 

Dukkan Maluman Mazhabobin sunyi ittifaqi akan cewa wadannan sune sharudan ingancin Sallar Janazah:

* Tsarki da alwala.

* Suturce Al'aurah.

* Kallon Alqiblah.


Amma Sha'aby da Ibnu Jareer sunce za'a iya yi ko ba tare da alwala ba.

Imam Shafi'iy da Abu Yusuf sunce Limami yana tsayawa ne adaidai kan mutum Namiji, ita kuma mace Liman zai tsaya ne adaidai tsakiyar ta.

Amma IMAMU MALIK DA IMAM ABU HANEEFAH Sunce Liman zai tsaya ne adaidai Qirjin Namiji, ita kuma mace zai tsaya ne adaidai adaidai tsakiyarta.


KABBARORINTA :

Kabbarori hudu ake yi asallar janazah abisa ittifakin Mazhabobin nan hudu.

Sai dai an ruwaito Kabbara 3 daga Imam Ibnu Sireen.

Sannan akwai wata ruwayar daga Abdullahi bn Mas'ud (rta) yace: "Manzon Allah (saww) yayi kabbara 9 abisa Janazah, Sannan yayi 7, Sannan yay 5, Sannan yayi 4. 

Kuyi ta kabbara mutukar Limanminku ya kabbara. Koda ya Qara abisa hudu to sallar ba ta 'baci ba".

Imamush-Shafi'iy yace Zaka cira hannuwanka zuwa kafadunka ayayin dukkan kabbarorin. Amma IMAMU MALIK DA IMAM ABU HANIFAH sunce ba zaka cira hannuwanka ba sai dai akabbarar farko kawai..

Karanta Fatiha bayan kabbarar farko, Farilla ne awajen Imam Shafi'iy da Imamu Ahmad. Amma Imamu Malik da Abu Haneefa Sunce BA ZAKA KARANTA KOMAI BA DAGA CIKIN AYOYIN ALQUR'ANI.

Sannan ana yin Salatun Nabiyyi (saww) sannan kuma sai Addu'a ga mamacin da sauran al'ummar musulmi abayan Kabbara ta biyu data uku da ta hudu a jere..

Sannan mutum zai yi sallama ne guda biyu abisa Mazhabobi uku. 

Amma Hanbaliyya sunce Sallama daya zaka yi a damanka.

Aduba Thamrud-dany Babin Sallar Janazah da kuma Rahmatul-Ummah shafi na 81.

WALLAHU A'ALAM..


Article Translation in English Language.

Funeral is a prayer offered to the deceased when he died before he was taken to the grave. All the Scholars of the Sects agreed that the JANAZAH is a FARILLAH of KIFAYAH. (that is the kind of decree that someone can take away from someone else). 

However, it was narrated from Asbag (one of the disciples of Imam Malik) that he is the Sunnah. The Funeral prayer can be performed at any time, day or night, said IMAM SHAFI'IY (RAH). 
But IMAM AHMAD AND IMAM ABU HANEEFAH (RAH) said that it is makruh to pray Janazah at these three times.

1. after Fajr prayer until sunrise. 
2. After the noon prayer until sunset.. 
3. When the Friday Imam gets on the pulpit and preaches. 
As for Imam Malik (RAH), he said that the Janazah prayer can be performed at any time except when the sun rises and when it sets, he said that it is Makruhi.

TERMS AND CONDITIONS: 
All the scholars of the sects agreed that the following are the conditions for the validity of the Janazah prayer: 
* Purity and ablution. 
* Dress properly. 
* Looking at Alqiblah.

But Sha'aby and Ibn Jareer say that it can be done without ablution. 

Imam Shafi'i and Abu Yusuf said that the Imam stands at the head of the male person, and the female Imam stands at the middle of her. 

But IMAM MALIK and IMAM ABU HANEEFAH said that the iman will stand at the chest of a man, and the woman will stand at the middle of it. 

ITS CAPABILITIES: 
Four Kabbara are used for the funeral according to the consensus of the four sects. 

However, Kabbara 3 was narrated from Imam Ibnu Sireen. 
Then there is a narration from Abdullah bin Mas'ud (rta) who said: 
"The Messenger of God (saww) did 9 times Kabbara during Janazah, then he did 7, then he did 5, then he did 4. four times, Keep Kabbara  as much as iman did, even if he did more than four times, then the prayer will not be "invalid".

Imamush-Shafi'iy said: "You will raise your hands to your shoulders during Kabbara for funeral prayer." 
But IMAM MALIK AND IMAM ABU HANIFAH said that you will not remove your hands except for the first kabbara.. 
Read Fatiha after the first Kabbara, it is Farilla during the mazhab of Imam Shafi'i and Imam Ahmad. 
But Imam Malik and Abu Haneefa said that you will not read anything from the verses of the Qur'an. 

Then the Salawat of the Prophet (peace be upon him) is performed and then Dua'a for the deceased and the rest of the Muslim community after the second, third and fourth Kabbara in a row. Then a person will say two salams according to the three sects.

But the Hanbaliyya say that you will make one Salam on your right. 

For reference:
Read Thamrud-dany Chapter of Janazah Prayer and Rahmatul-Ummah page 81.

WALLAH AALAM..

SHARE THIS

Author:

Etiam at libero iaculis, mollis justo non, blandit augue. Vestibulum sit amet sodales est, a lacinia ex. Suspendisse vel enim sagittis, volutpat sem eget, condimentum sem.

0 comments: