Saturday, December 7, 2024

Wace shekara akayi yakin Badar?

Wace shekara akayi yakin Badar?

A gwabza yakin badar ne a ranar 17 ga watan Ramadan shekaru biyu kacal da yin Hijran Annabi MUHAMMAD (S.A.W) daga Makka zuwa Madina.
Nasarar da Musulmi suka samu akan kafirai a yakin Badr karkashin jagorancin Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi da zuriyarsa, ya kasance nasara mai matukar muhimmamci a tarihin musulunci, Kasancewar shine yaki na farko da rundunar Musulunci ta fuskanci kafirci, Wanda kafiran makka Suka yi ma tanaji kwarai da gaske.

Hakika yakin badar ya kasance tubali na cigaban kafuwar musulunci duba da yadda Allah Madaukakin sarki ya kawo karshen manya-manyan kafiran makka wadanda Suka kuntatawa Annabi (S.A.W) Wanda Sai da Allah ya umurce shi da yin hijra zuwa Madina.

Kwamandojin Musulunci a wannan ranar karkashin jagoranci shugaban Halitta (S.A.W) 
Ali ibn Abi Talib
Zubayr ibn al-Awwam
al-Miqdad bin 'Amr
Hamza ibn Abd al-Muttalib
Umar bn kattab
'Ubaydah bin al-Harith
Bilal ibn Rabah al-Habashi

Sai bangaren kafiran makka karkashin jagorancin Amr ibn Hisham Wanda a kafi sani da Abu jahal sune
Utbah ibn Rabi'ah 
Umayyah ibn Khalaf 
Shaybah ibn Rabi'ah 
Walid ibn Utbah 
Uqba ibn Abi Mu'ayt 

Yawan kafiran makka su 1000 da dawakai 70 da rakuma 170
Yayin da musulmai ke da yawan mutane 313 da dawakai 2 da rakuma 70

A wannan ranar Manzon Allah (S.A.W) yayi addu'a Inda yake cewa 

"Ya Allah wannan Quraishawa wadanda Suka kasance masu girman kai da kalubalantarKa da kuma karyata Manzonka, Ya Allah ka ba mu nasarar da ka alkawarta mani, Ya Allah ka sanya ma wannan rundunar alheri da safiya. 

Kuma ya zo a wata ruwaya cewa, da ya ga tarin mushrikan makka sun tunkaro, 'ya fuskanci alqibla yana mai cewa: 
“Ya Allah ka cika abin da ka yi mini alkawari, ya Allah idan an halakar da wannan rundunar, ba zaka samu wadanda zasu bauta maka ba".

Allah Madaukakin sarki ya ba musulmai nasara akan kafiran makka a wannan yaki Inda aka kashe kafirai 70 tare da kama 70  yayinda musulmai 14 Suka yi shahada a wannan ranar da Allah (S.W.T) ya tabbatar da alkawarinsa ga masoyinsa (S.A.W).

Article Translation in English Language.

The Battle of Badr was fought on the 17th of Ramadan, just two years after the Prophet MUHAMMAD (S.A.W) migrated from Mecca to Medina. 
The victory of the Muslims against the infidels in the battle of Badr under the leadership of the Messenger of God, peace and blessings of God be upon him and his descendants, was a very important victory in the history of Islam. 

The unbelievers of Makkah were very arrogant. Indeed, the battle of Badr was a building block for the development of Islam, considering how God the Almighty put an end to the Meccan infidels who persecuted the Prophet (S.A.W), who was commanded by God to migrate to Medina.


Islamic commanders on this day under the leadership of Halitta (S.A.W) 
Ali ibn Abi Talib 
Zubayr ibn al-Awwam 
al-Miqdad bin 'Amr 
Hamza ibn Abd al-Muttalib 
Umar bin Kattab 
'Ubaydah bin al-Harith 
Bilal ibn Rabah al-Habashi 

Then the unbelievers of Makkah under the leadership of Amr ibn Hisham who is better known as Abu Jahal are 
Utbah ibn Rabi'ah 
Umayyah ibn Khalaf 
Shaybah ibn Rabi'ah 
Walid ibn Utbah 
Uqba ibn Abi Muayt 
The number of unbelievers in Makkah is 1000, 70 horses and 170 camels While Muslims have 313 people, 2 horses and 70 camels. 

On this day, the Messenger of God (S.A.W) prayed "O Allah, this Quraysh who were proud to challenge You and deny Your Messenger, O Allah, give us the victory you promised me, O Allah, grant this army a good morning."

And it came in a narration that, when he saw a group of Meccan polytheists approaching, he faced the Qibla and said: 

"O God, fulfill what you promised me, O God, if this army is destroyed, you will not find those who will serve you". 

Allah Almighty gave the Muslims victory over the infidels of Makkah in this war where 70 infidels were killed and 70 were captured while 14 Muslims were martyred on this day when Allah (S.W.T) confirmed his promise to his beloved (S.A.W).


SHARE THIS

Author:

Etiam at libero iaculis, mollis justo non, blandit augue. Vestibulum sit amet sodales est, a lacinia ex. Suspendisse vel enim sagittis, volutpat sem eget, condimentum sem.

0 comments: