An haifi Sheikh Dahiru Usman Bauchi a ranar 29-Dhu al-Hijjah-1345 Wanda yayi daidai da 29 June 1927 miladiyan Annabi Isha (AS) a Garin Bauchi dake arewa maso gabashin Najeriya.
Sheikh Dahiru Bauchi yayi karatun Alkur'ani a wajen mahaifinshi Alhaji Usman ya haddace Alkur'ani a wajensa kuma yayi sauran karatunsa a wajen wasu fitattun Malamai a lokacin kamar Sheikh Tijani Usman Zangon Bare-bari da Sheikh Abubakar Atiku da Sheikh Abdulqadir Zaria.
Sheikh Dahiru Usman Bauchi Yana da 'ya’ya 95 da jikoki 406 da tattaba-kunne 100. Daga cikin wannan adadin, ’ya’yansa 77 ne da jikoki 199 da kuma tattaba-kunne 12 ne suka haddace Alkur’anin mai girma.
daga cikin matayen da ya aura akwai 'yar shehunsa sheikh Ibrahim inyass haka zalika Sheikh Dahiru Usman Bauchi shine. Mataimakin Shugaban Majalisar Kolin Malamai dake bayar da Fatawar Musulunci a Najeriya sannan babban jigo ne a Darikar Tijjaniya a Najeriya da ma Afirka kuma khalifan Sheikh Ibrahim inyass (Wanda shine khalifan Ahmadu Tijjani, Wanda ya kafa darikar tijjaniya).
Article Translation in English Language.
Sheikh Dahiru Usman Bauchi was born on 29-Dhu al-Hijjah-1345 which is equivalent to 29 June 1927 AD in Bauchi town located in northeastern Nigeria.
Sheikh Dahiru Bauchi studied the Qur'an with his father Alhaji Usman and memorized the Qur'an with him and did his other studies with some prominent scholars at that time such as Sheikh Tijani Usman Zangon Bare-bari, Sheikh Abubakar Atiku and Sheikh Abdulqadir Zaria.
Sheikh Dahiru Usman Bauchi has 95 children, 406 grandchildren and 100 grandchildren. Out of this number, 77 of his children, 199 grandchildren and 12 grandchildren have memorized the Holy Quran.
Among the wives he married there was the daughter of his sheikh, Sheikh Ibrahim inyass, as well as Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
The Vice President of the Supreme Council of Scholars that gives Islamic Fatawa in Nigeria and is a leading figure in the Tijjaniya sect in Nigeria and Africa and the caliph of Sheikh Ibrahim Inyass (who is the caliph of Ahmadu Tijjani, the founder of the Tijjaniya sect)
0 comments: