Tuesday, December 3, 2024

Prof Isa Ali Pantami biography

 Tarihin Prof Isa Ali Pantami

An haifi Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami a ranar 20 ga watan Oktobar 1972 a unguwar Pantami dake jihar Gombe a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Isa Pantami ya kasance ‘da ga Mallam Ali Ibrahim Pantami, mahaifiyarshi kuwa itace Malama Amina Umar Aliyu.

Ya fara karatun Al-Qur’ani a makarantar Allo kafin daga bisani ya shiga makarantar Firamare ta ‘Pantami Primary School’ inda a nan ne ya samu shaidar kammala karatun firamare, ya kammala karatun sakandire a makarantar Sakandire ta Kimiyya ta ‘Government Science Secondary School, Gombe.

Daga nan ne ya samu shigar jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) dake jihar Bauchi, inda a nan ne ya samu damar kammala karatun Digiri a fannin Fasahar Kwafuta a shekarar 2003 tare da samun Digiri na 2 duk a fannin, a shekarar 2008. Pantami ya kammala karatun Digirin-digirgir a jami’ar Robert Gordon dake Aberdeen a kasar Sukotlan.

Ya fara aiki a jami’ar ATBU, inda yake koyar da ‘Information Technology’ kafin daga bisani ya koma Jami’ar Musulunci dake Madinah a matsayin shugaban Rubutun Fasaha a shekarar 2014.

A shekarar 2016, Pantami ya ajiye koyarwa, inda a nan ne shugaba Muhammad Buhari ya nada shi ya zama shugaban hukumar ‘NITDA’ a ranar 26 ga watan Satumbar 2016.
Ya kasance babban malamin addinin Musulunci na sama da shekaru 20, ya kasance limamin sallah Juma’a a Najeriya da kasar Birtaniya.

Source: Jaridar Punch

Article Translation in English Language.

Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami was born on the 20th day of October 1972 in Pantami area in Gombe state in North Eastern Nigeria. 

Isa Pantami was born to Mallam Ali Ibrahim Pantami, and his mother was Mallama Amina Umar Aliyu. 

He started studying Al-Qur'an at Allo school before he joined Pantami Primary School where he got his primary school certificate and finished his secondary education at Government Science Secondary School. , Gombe. From there, he was admitted to Abubakar Tafawa Balewa University (ATBU) in Bauchi State, where he was able to complete his degree in Computer Technology in 2003 and obtained a 2nd Degree in the field in 2008. 

Pantami completed his PhD studies at Robert Gordon University in Aberdeen, Scotland. He started working at ATBU University, where he taught 'Information Technology' before he moved to the Islamic University in Madinah as the Head of Technical Writing in 2014. 

In 2016, Pantami retired from teaching, where President Muhammad Buhari appointed him to be the chairman of NITDA on September 26, 2016. 

He is a leading Islamic teacher for over 20 years, he was a Friday prayer leader in Nigeria and the UK. 

Source: Punch newspaper

SHARE THIS

Author:

Etiam at libero iaculis, mollis justo non, blandit augue. Vestibulum sit amet sodales est, a lacinia ex. Suspendisse vel enim sagittis, volutpat sem eget, condimentum sem.

0 comments: