Thursday, December 26, 2024

Kiran sallah a rubuce: Yadda ake kiran sallah da iqama

 


Kiran sallah ibada ce da akeyi a lokacin shigan sallar farilla da nufin sanar da al'ummar Musulmi lokacin sallah yayi, Kiran sallah da tayar da iƙamah yana cikin mahimman abubuwa da suke ƙara bayyana girma da buwayar addinin musulunci.

HUKUNCIN KIRAN SALLAH.

Malamai sunyi magana biyu akan hukuncin yin kiran salla, wasu daga ciki suka ce yin kiran salla wajibi ne  akan dukkan musulmi, amma idan wani yayi ya ɗaukewa ragowar, wasu suka ce sunna ne mai ƙarfi, ya zama ana yin kiran salla, a kowane gari, a kowane masallaci.
Sallolin farilla kawai ake yiwa kiran salla, da sallar juma'a. 
Sallolin da ba'a yi musu kiran salla sune, sallar idi biyu, da sallar rokon ruwa, da sallar kusufin wata da rana, da sallar jana'iza da sallar wutri.
Baa kiran salla sai lokaci ya yi, in banda sallar asuba, wacce ake yi mata kiran salla biyu, daya kafin lokaci, na biyu bayan lokaci ya yi. Saboda hadisin Bilal da Manzon Allah saw yace, Bilal yana kiran salla da daddare don haka ku ci ku sha, har sai kunji kiran salla daga Abdullahi Ɗan Ummu maktum, domin shi makaho ne baya kiran salla har sai an ce masa alfijir ya keto. 
Bukhari da Muslim sun ruwaito hadisin. 
Za'a iya kiran salla domin rama sallar da ta tsere, 
Mutum ɗaya idan zai yi salla, zai iya kiran salla 
Idan mutum zai haɗa salla biyu, kiran salla sau ɗaya ya wadatar. 
Mace ba zata yi kiran salla ba, sai idan mata ne kawai a wajan, babu namiji da zai jiyo muryar ta, kamar yadda Al Imam Nawawiy, ya faɗa da fatawar Imam malik da Imam shafii da wata riwaya daga Al imam Ahmad.

SIIGAR KIRAN SALLAH

 Kiran salla yazo da siga kala-kala, akwai yadda yazo a hadisin Abi Mahzurah da hadisan Bilal, duk wanda aka ɗauka ya wadatar, amma duk wanda zai zama ladani wajibi yaje wajan malamin addini ya koya masa yadda ake kiran sallah, domin mafi yawan masu kiran sallah suna kurakurai da yawa, akwai buƙatar a dinga shiryawa ladanai bita akan kiran sallah, da domin a ɗinka gudanar da komai akan ilmi.

A INA AKE SAKA ASSALATU KHAIRUN MINAL NAUMI?

Acikin kiran Sallah na asuba zaa ƙara Assalatu Khairun minan naumi, wasu malamai sunce a cikin kiran salla na farko zaa faɗa, kuma wasu malamai sunce a cikin kiran salla na biyu, wasu malamai sunce a cikin ko wacce za ayi , wasu sunce an bayar da zaɓi zaa iya sawa a na farko ko a na biyu, amma abinda yafi rinjaye shine a cikin kiran sallah na farko za ayi assalatu. 
Duba littafin Al fiqhu al mu saffa na Abu malik.

SUNNONIN MAI KIRAN SALLAH:
Sunnanin mai kiran salla, anso ga wanda zaiyi kiran salla, ya kula da waɗannan sunnoni. 
1, Idan zai kira sallah ya zama yana da Alwala. 
2,  yayi kiran salla a tsaye. 
3, Ya fuskanci alƙibla, 
4,  Yasa yatsunsa a cikin kunne ya kama kunnansa. 
5,  Ya dinga waywaye hagu da dama lokacin faɗar hayya alal salah. 
6, Ya ɗaga murya ya kyautata muryar sa. 
7, Ya zama a wajan masallaci idan da dama, kuma ya hau guri mai tudu idan babu sifika.

WANDA YA JIYO KIRAN SALLAH 
Abubuwan da suka shafi wanda ya jiyo kiran sallah
1, Ya faɗi abinda ya ji mai kiran salla yana faɗa 
2,  Amma a wajan hayya alal sala sai yace lahaula wala ƙuwwata illa billah, da wajan faɗar hayya alal falah, sai yace lahaula wala ƙuwwata illa billah. 
3,  Yayi wa Annabi saw salati. 
4. Yayi wannan addu'ar ta roƙawa Annabi saw wasila da fadhila. 
5,  Yayi addu'a ta neman buƙatar duniya da lahira. 
6,  Duk wanda yake cikin masallaci, kada ya fita bayan an kira sallah, sai bayan an gama salla, sai idan alwalar sa ta warware.

SUNNONIN TAFIYA MASALLACI. 
Wanda zai tafi masallaci ya kula da wannan sunnoni 
Ya tafi da Alwala 
Yana zikrin tafiya wajan salla 
Ya tafi cikin nutsuwa, da hankali. 
Idan zai shiga masallacin ya shiga da ƙafar dama.
Amma wajan cire takalmi ya fara cire ƙafar hagu, 
Yayi addu'ar shiga masallaci. 
Yayi nafila kafin ya zauna. 
A duba littafin Alfiqhu Almusaffa na Abu malik daga shafi na 90 zuwa na 96.

Allah ya bamu dacewa akan ilmi da aiki dashi saboda Allah.

Yadda ake kiran sallah shi ne, 

“Allahu Akbar, 
Allahu Akbar, 
Allahu Akbar, 
Allahu Akbar, 
Ashhadu An La’ilaha ilal Lah, 
Ashhadu an la’ilaha ilal lah, 
Ashhadu anna Muhammadan Rasulullah, 
Ashhadu anna Muhammadan Rasulullah, 
Hayya alal Salah, 
Hayya alal Salah, 
Hayya alal falah, 
Hayyah alal falah, 
Allahu Akbar, 
Allahu Akbar, 
La’ilaha ilal Lahu” 


Yadda ake Iqama : 


“Allahu Akbar, 
Allahu Akbar, 
Ashhadu An La’ilaha ilal Lah, 
Ashhadu anna Muhammadan Rasulullah, 
Hayya alal Salah, 
Hayya alal falah, 
Qad Qamatus Salatu, Qad qamatus Salah, 
Allahu Akbar, 
Allahu Akbar, 
La’ilaha ilal Lahu”.

Article Translation in English Language.

The call to prayer is an act of worship that is performed during the obligatory prayer with the intention of informing the Muslim community when it is time to pray.

RULINGS FOT CALLING TO PRAYER:

Scholars have two opinions on the decision to call for prayer, some of them said that calling for prayer is obligatory for all Muslims, but if someone takes away the remains, others say that it is a strong sunnah, so it is called for prayer, in every town. , in every mosque. Only obligatory prayers are called for prayer, and Friday prayers. 

The prayers that are not called for prayer are, the two Eid prayers, the prayer of asking for water, the eclipse of the moon and the day, the funeral prayer and the Wutri prayer. 
He does not call for prayer until the time has come, except for the morning prayer, for which there are two calls for prayer, one before the time and the second after the time has come. 

Because of the hadith of Bilal that the Messenger of God, may God bless him and grant him peace, said, Bilal calls for prayer at night, so eat and drink until you hear the call for prayer from Abdullahi son of Umm Maktum, because he is blind and does not call for prayer until he is told that dawn has broken. 

Bukhari and Muslim narrated the hadith. A prayer can be called to make up for a missed prayer, If a person is going to pray, he can call for prayer If one is going to combine two prayers, calling the prayer once is sufficient. 
A woman will not call for prayer, unless there is only a woman in the room, no man will hear her voice, as Al Imam Nawawiy said with the fatwa of Imam Malik and Imam Shafi'i and a narration from Al Imam Ahmad.

A VERSION OF THE CALL TO PRAYER:

The call to prayer comes in different forms, there is a way of it in the hadith of Abi Mahzurah and the hadith of Bilal, whoever is considered is sufficient, but whoever will be rewarded must go to the religious teacher and teach him how to call the prayer, because most of the There are many mistakes in the call to prayer, there is a need to prepare a review on the call to prayer, and to conduct everything based on knowledge. 

WHERE IS THE ASSALATU KAIRU MINAL NAUMI? 
In the morning prayer call, Assalatu Khairun minan naumi will be added. It can be worn in the first or the second, but the most important thing is that in the first call to prayer, assalat will be done. See the book Al fiqhu al mu saffa by Abu Malik. 

SUNNAH OF THE PRAYER CALLER: 

The sunnah of the person calling for prayer, and whoever is going to call for prayer, should take care of these sunnahs. 
1, If ​​he calls for prayer, he must have ablution. 
2, he called for standing prayer. 
3, He faced the direction, 
4, He put his fingers in the ear and caught it. 
5, He keeps looking left and right when saying hayya alal salah. 
6, He raised his voice and improved his voice. 
7, He sits on the side of the mosque if there is a chance, and he climbs a hill if there is no speaker.

WHO HEARD THE CALL TO PRAY Things that concern the one who hears the call to prayer 
1, He said what he heard the prayer caller saying 
2, But when saying haya al-salah, he said lahaula wala kuwwata illah billah, and when saying haya al-falah, he said lahaula wala kuwwata illah billah. 
3, He prayed for the Prophet, peace be upon him. 
4. He said this prayer asking the Prophet, may God bless him and grant him peace, for blessings and blessings. 
5, He prayed for the needs of this world and the hereafter. 
6, Whoever is in the mosque, should not leave after the prayer is called, unless the prayer is finished, unless his ablution is resolved. 

GOING TO MOSQUE . 
Whoever goes to the mosque should pay attention to this sunnon He went with ablution He recites walking while praying He went quietly and calmly. 
If he is going to enter the mosque, he should enter with the right foot. But when he took off his shoes, he began to take off his left foot, He prayed to enter the mosque. He nodded before he sat down. 

SOURCES:
fin the book Alfiqhu Almusaffa by Abu Malik from page 90 to 96. 
May God give us the ability to learn and work with it.

SHARE THIS

Author:

Etiam at libero iaculis, mollis justo non, blandit augue. Vestibulum sit amet sodales est, a lacinia ex. Suspendisse vel enim sagittis, volutpat sem eget, condimentum sem.

0 comments: