Monday, December 2, 2024

Fassarar salatul ibrahimiyyah

 Fassarar salatul ibrahimiyyah


Salatul ibrahiyyah salatin Annabi ne da Al'ummar musulmi ke yi domin gaisuwa da jinjina ga Shugaban halitta Annabi Muhammad (S.A.W). Kuma shine salatin da Annabi ya koyar da sahabbansa a lokacin rayuwasa, duk da cewa akwai tarin salatin da ake yi wa Annabi (S.A.W) wanda yin Hakan bai saba ma Shari'a ba, ma'ana shari'ar musulunci bata ka'idance cewa dole Sai salatul ibrahimiyyah Kawai za'ayi wa Annabi ba, zaka Iya yin ma Annabi kowanne irin salati matukar lafuzansa baici Karo da koyarwar musulunci.

Kasantuwar ana yin salatin ne a cikin harshhen larabci Kamar yadda Annabi (S.A.W) ya koyar, saboda haka ne muka kawo maku fassaran salatul ibrahimiyyah a cikin Hausa domin samun lafuzzan dake cikinsa.

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَىٰ مُحَمَّدٍ وَعَلَىٰ آلِ مُحَمَّدٍ ❁ كَمَا صَلَّيْتَ عَلَىٰ إِبْرَاهِيمَ وَعَلَىٰ آلِ إِبْرَاهِيمَ ❁ إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ
"Allāhumma ṣalli ʿalā Muḥammadin wa ʿalā āli Muḥammad(in), kamā ṣallayta ʿalā Ibrāhīma wa ʿalā āli Ibrāhīm(a), innaka Ḥamīdun Majīd".

"Ya Allah muna rokonka ka daukaka darajar Annabi Muhammadu da iyalansa, kamar yadda ka daukaka darajar Annabi Ibrahim, da iyalansa. Lallai Kai ne wanda ya cancanci a yabe shi da godiya, kuma wanda ake wa tasbihi". 

اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَىٰ مُحَمَّدٍ وَعَلَىٰ آلِ مُحَمَّدٍ ❁ كَمَا بَارَكْتَ عَلَىٰ إِبْرَاهِيمَ وَعَلَىٰ آلِ إِبْرَاهِيمَ ❁ إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ
"Allāhumma bārik ʿalā Muḥammadin wa ʿalā āli Muḥammad(in), kamā bārakta ʿalā Ibrāhīma wa ʿalā āli Ibrāhīm(a), innaka Ḥamīdun Majīd".

"Ya Allah muna rokonka ka yi salati ga Annabi Muhammadu da iyalansa kamar yadda Ka yi salati ga Annabi Ibrahim, da iyalansa, Lallai Kai ne wanda ya cancanci a yabe shi da godiya, kuma wanda ake tasbihi". 


Salatul ibrahimiyyah na 2

Version 2
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَىٰ مُحَمَّدٍ وَعَلَىٰ آلِ مُحَمَّدٍ ❁ كَمَا صَلَّيْتَ عَلَىٰ إِبْرَاهِيمَ وَعَلَىٰ آلِ إِبْرَاهِيمَ ❁ وَبَارِكْ عَلَىٰ مُحَمَّدٍ وَعَلَىٰ آلِ مُحَمَّدٍ ❁ كَمَا بَارَكْتَ عَلَىٰ إِبْرَاهِيمَ وَعَلَىٰ آلِ إِبْرَاهِيمَ فِي الْعَالَمِينَ ❁ إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ

Allāhumma ṣalli ʿalā Muḥammadin wa ʿalā āli Muḥammad(in), kamā ṣallayta ʿalā Ibrāhīma wa ʿalā āli Ibrāhīm(a), wa bārik ʿalā Muḥammadin wa ʿalā āli Muḥammad(in), kamā bārakta ʿalā Ibrāhīma wa ʿalā āli Ibrāhīm(a) fi l-ʿālamīn(a), innaka Ḥamīdun Majīd.

O Allah, send prayers upon Muhammad and upon the family of Muhammad just You as have sent prayers upon Ibrahim and upon the family of Ibrahim, and bless Muhammad and the family of Muhammad just as You have blessed Ibrahim and the family of Ibrahim in all the worlds, verily You are the Praiseworthy the Glorious.

Ya Allah ka yi salati ga Muhammadu da alayen Muhammadu kamar yadda ka yi salati ga Ibrahim da alayen Ibrahim, kuma ka yi salati ga Muhammadu da alayen Muhammadu, kamar yadda Ka yi salati ga Ibrahim da alayen Ibrahim a cikin dukkan halittu baki daya. tãlikai, lalle ne Kai, Gõdadde ne Mabuwãyi.

Article Translation in English Language.

Salatul Ibrahiyyah is the prayer of the Prophet that the Muslim community does to greet and greet the leader of creation, Prophet Muhammad (S.A.W). 

And it is the salat that the Prophet taught his companions during his lifetime, even though there are many salats that are performed for the Prophet (S.A.W) which does not contradict the Shari'a, meaning that the Islamic Shari'a does not rule that It is necessary to say Salatul Ibrahimiyyah only for the Prophet. 

Salat is done in Arabic language as the Prophet (S.A.W) taught, that is why we have brought you the translation of Salatul Ibrahimiyyah in Hausa to get the words in it.

SHARE THIS

Author:

Etiam at libero iaculis, mollis justo non, blandit augue. Vestibulum sit amet sodales est, a lacinia ex. Suspendisse vel enim sagittis, volutpat sem eget, condimentum sem.

0 comments: