Monday, December 2, 2024

Dua for entering the Masjid and leaving


Allahummaftahli Abwaba Rahmatika, this is a prayer that the Messenger of God (S.A.W) taught when a person is going to enter the mosque as mentioned in his hadith. 

May the Messenger of God, peace and blessings of God be upon him, teach us to pray before starting and completing our daily transactions in order to obtain protection from the devils in the open and hidden, as well as some prayers to obtain blessings and the will of the lord the creator. 

Therefore, it is recommended that when a person enters the mosque, he should try to recite this Du'aar in order to receive the grace and approval of God when he performs his obligatory prayer. 

It is in the hadith of the Messenger of God (S.A.W) that Abu Usaid (R.A) narrated that: If one of you will enter the mosque and say: "O Allah! Open the doors of Your mercy for me"; and when he goes out he says: 
'Oh God! I am asking You for Your grace'.


May God Almighty grant us power and zeal to implement what we have learnt, Ameen

Article Translation in Hausa Language.

Allahummaftahli Abwaba Rahmatika, wannan Addu'a ce Wanda manzon Allah (S.A.W) ya koyar idan mutum zai shiga masallaci kamar yadda yazo a cikin hadisinsa. 

Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya koyar da mu Addu'o i kafin farawa da kammala Mu'amalolinmu na rayuwa domin samun kariya daga shaidanun fili da na boye haka zalika wasu Addu'o in domin samun falala ne da yardar ubangiji mahalicci.

Don haka ana so idan mutum zai shiga Masallaci yayi kokari ya rinka karanta wannan Addu'ar domin samun falala da yardan Allah a lokacin da zai gudanar da sallar sa ta farilla.

Yazo a cikin hadizin manzon Allah (S.A.W) wanda Abu Usaid (R.A) ya ruwaita cewa:

عَنْ أَبِي أُسَيْدٍ، – قَالَ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم ‏ “‏ إِذَا دَخَلَ أَحَدُكُمُ الْمَسْجِدَ فَلْيَقُلِ اللَّهُمَّ افْتَحْ لِي أَبْوَابَ رَحْمَتِكَ ‏.‏ وَإِذَا خَرَجَ فَلْيَقُلِ اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ فَضْلِكَ

Idan dayanku zai shiga masallaci ya ce: "Ya Allah! Ka bude mini kofofin rahamarKa"; kuma idan zai fita ya ce: ‘Ya Allah! Ina rokonKa falalarka. -Muslim


Allahummaftahli Abwaba Rahmatika

اللَّهُمَّ افْتَحْ لِيْ أَبْوَابَ رَحْمَتِكَ

Ya Allah! Ka bude mini kofofin rahamarKa. 

Allah madaukakin sarki ya bamu ikon aika tawa Amin.


SHARE THIS

Author:

Etiam at libero iaculis, mollis justo non, blandit augue. Vestibulum sit amet sodales est, a lacinia ex. Suspendisse vel enim sagittis, volutpat sem eget, condimentum sem.

0 comments: