Annabi Muhammad (S.A.W) an haife shi a shekara ta 570 bayan haihuwar Annabi Isa (AS) a Garin Makka ta Kasar Saudi Arabia, ya kuma yi wafati a ranar 8 ga watan Yuni shekaran 632 a birnin Madina na Kasar Saudi Arabia.
Shi ne ya kafa Musulunci Addinin musulunci wanda yawansu yakai biliyan 1.9 na Al'ummar Duniya biliyan 8 a halin yanzu.
Annabi Muhammad (S.A.W) ya kasance abun koyi ga dukkan musulmin duniya.
Mahaifinshi Abdullahi ya rasu tun kafin a haife Shi a lokacin mahaifiyasa Nana Aminatu na dauke da cikinsa wata 6.
Bayan watanni uku da rasuwar Abdullahi Sai Nana Aminatu ta haifi Annabi Muhammad (S.A.W), Haihuwuwar ma'aiki (S.A.W) yazo da mu'ijizoji da abubuwan al'ajabi a wancan lokacin Kamar yadda yazo a tarihi, Alamonin bayyanarsa ya tun daga samun cikinsa har zuwa lokacin da yazo duniya Nana Aminatu ta ga Abubuwan Al'ajabin da bata saba gani ba.
bayan haihuwar Annabi (S.A.W) mahaifiyarshi ta bayar da shi shayarwa ga Halimah bint Abi Dhuayb, saboda a wancan lokacin labarawa na bayar da jariransu shayarwa domin su samu nagartattun tarbiya da halaye.
Bayan ya shekara 6 a wajan sayyada Halima, nana aminitu ta karbo Shi domin takai ziyara wajen danginta garin Yasrib (yanzu Madina) inda suka tafi tare Annabi (S.A.W), suna Kan hanyarsu ta dawowa gida tare da bawanta, Umm Ayman, Sai Nana Aminatu ta kamu da rashin lafiya inda ta rasu a kauyen Al-Abwa lokacin Annabi na da Shekaru 6 a duniya.
Article Translation in English Language.
Prophet Muhammad (S.A.W) was born in the year 570 after the birth of Prophet Jesus (AS) in Makkah, Saudi Arabia, and he died on June 8, 632 in Medina, Saudi Arabia.
He is the founder of Islam, the religion of Islam, whose number is 1.9 billion of the world's 8 billion people at the moment.
Prophet Muhammad (S.A.W) was a role model for all Muslims around the world. His father Abdullahi died before he was born when his mother Nana Aminatu was 6 months pregnant with him.
Three months after the death of Abdullahi, Nana Aminatu gave birth to Prophet Muhammad (S.A.W), the birth of the servant (S.A.W) came with miracles and wonders at that time.
Until the time she came to the world, Nana Aminatu saw wonders that she had not seen before.
After the birth of the Prophet (S.A.W), his mother gave him breastfeeding to Halimah bint Abi Dhuayb, because at that time, Arabs gave their babies breastfeeding so that they would have good education and manners.
When He was 6 years old, Prophet's Mother, Nana Aminatu took Him from Halima to visit her family in the town of Yasrib (now Medina) where they went with the Prophet (S.A.W), on their way back home with her servant, Umm Ayman, then Nana Aminatu She fell ill and died in the village of Al-Abwa when the Prophet was 6 years old.
0 comments: