Saturday, December 7, 2024

Abubuwan da suke karya azumin nafila ko farilla.

Abubuwan da suke karya azumin nafila ko farilla.

Azumi dai daya ne daga cikin shika-shikan musulunci guda biyar Wanda yake nufin kamewa daga duk barin cin wani abu ko sha ko Kuma yin jima'a tun kafin fitowar alfijir har zuwa fatuwar rana.

Saboda haka yakamata duk Musulmi ya sani cewa azumi babban ibada ne Wanda ya wajjaba akanshi indai ya balaga kamar yadda sallah da sauran shika-shikan musulunci suka wajaba akansa.

Don hakane manzon Allah (S.A.W) ya gargadi duk Musulmi mai azumi da ya kiyaye abubuwan da zasu lalata ko karya mashi azuminsa domin ya guje ma shan yunwar banza da kuma fushin ubangiji ma halicci.

Wadannan sune abubuwan dake karya ma Musulmi azumin farilla ko na nafila.

* Cin abinci ko shan ruwa ko wani abu daban.

* Shan taba ko wani kayan maye.

* Yin jima'a.

* Fitar jinin haila kona biki.

* Shakan turare har zuwa makoshi

* Fitar maniyi ko maziyi ta hanyar sha'awa.


Sai dai malamai sunyi hukunce-hukuncen akan yadda mutum zai rama azuminsa idan ya karya. 

Misali idan Musulmi ya sha ko yaci abinci ko Kuma ya Shaka turare har yakai makoshinsa ko Kuma yaha taba ko kayan maye da gangar to zai rama azuminsa da ya karya sannan Kuma zai yi azumi 60 na kaffara, Amma idan bisa kuskure ne ko rashin lafiya ne yasa mutum karya azumi to zai rama adadin Wanda ya karya ne kawai.

Haka zalika idan mutum ya fitar da maniyi ko maziyi bisa kuskure misali ko ta hanyar mafarki, shima zai rama adadin Wanda yasha ne kawai Amma idan da gangar ne yayi sanadin fitar maniyi ko yayi jima'i to zai rama adadin Wanda yasha sannan Kuma yayi guda 60 na kaffara Amma wasu Malaman sunyi sabadi akan maziyi inda wasu ke cewa Sai anyi kaffara yayin da wasu ke cewa babu kaffara.

Saboda haka wajibin Musulmi ne ya kiyaye aikata duk wani abun da zai bata masa azuminsa ko yaya yake domin samun falalar dake cikinsa.

Article Translation in English Language.

Fasting is one of the five pillars of Islam which means refraining from eating, drinking or having sex from before dawn until sunset. 

Therefore, every Muslim should know that fasting is a great act of worship that is obligatory upon him when he reaches maturity, just as prayer and other Islamic rituals are obligatory upon him. 

That is why the Messenger of God (S.A.W) warned every Muslim who is fasting to avoid things that will destroy or break his fast so that he avoids hunger for nothing and the anger of the Lord. 

These are the things that break a Muslim's obligatory or voluntary fast. 

* Eating or drinking water or something else. 

* Smoking or other drugs. 

* Having sex. 

* Menstrual discharge. 

* Breathe the perfume up to the throat 

* Release of sperm or ejaculate through desire.

However, the scholars made rulings on how a person should make up for his fast if he breaks it. 

For example, if a Muslim drinks or eats food or smokes incense until it reaches his throat or consumes tobacco or intoxicants, then he will make up for his broken fast and then he will fast 60 days as an atonement. 

If a person breaks his fast, he will only compensate for the amount of the person who broke it. In the same way, if a person ejaculates by mistake, for example, or through a dream, he will also compensate for the amount of the person who had it. of atonement, but some scholars have argued against the husband, where some say that there is atonement, while others say that there is no atonement. 

Therefore, it is the duty of a Muslim to refrain from doing anything that will spoil his fast, no matter how it is, in order to get the blessings that are in it.



SHARE THIS

Author:

Etiam at libero iaculis, mollis justo non, blandit augue. Vestibulum sit amet sodales est, a lacinia ex. Suspendisse vel enim sagittis, volutpat sem eget, condimentum sem.

0 comments: