Sunday, December 8, 2024

Abubuwan Da Suke Karya Alwala

Mazhabar malikiyya ta kasa abubuwan da suke warware alwala izuwa gida biyu : hadasi da kuma sababan hadasin

Hadasi guda biyar ne, gudu uku suna fita daga gaban mutum sune : maziy, wadiy da kuma bawali (fitsari) gaba daya ukun ana musu tsarki kamar yadda ake tsarkin fitsari, guda biyu kuma suna futa ta baya sune: bayan gida da kuma tusa, duka wadannan hukuncin su daya ne idan kana da alwala daya ya same ka to alwalar ka ta karye sai ka sake wata. 

Sai kuma sababan hadasin sune kamar : bacci lokacin da kake da alwala, shima baccin ya rabu izuwa gida hudu. 


- Bacci mai tsayi kuma mai nauyi wannan baccin yana karya alwala. 

- Bacci mara tsayi wanda ba'a dade ana yi ba amma kuma mai nauyi ne, shima wannan baccin yana karya alwala. 

- Bacci mara tsayi kuma mara nauyi wannan baccin baya karya alwala. 

- Bacci mai tsayi mara nauyi shi kuma anso a sake alwala, amma alwalar bata karye ba. 

Daga kuma sababan da suke karya alwala akwai :  gushewar hankali idan kana da alwala sai hauka ya same ka alwalar ka ta karye, ko farfadiya, ko maye kana da alwala kasha kayan maye har suka gusar da hankalin ka alwalar ka ta karye. 

Haka zalika alwala tana karyewa da yin ridda kana da alwala ka fadi abinda zai fitar dakai daga musulunci (ridda) to alwalar ka ta karye, da kuma kokwanto a cikin hadasi, misali kayi kokwanton kayi fitsari amma baka tabbatar kayi tsarki ko bakai ba wannan ma yana lalata alwala har sai kazo da abinda kake kokwanto a cikin sa. 

Alwala tana karyewa idan mutum ya taba gaban sa da hannun sa babu wani abu tsakani kamar wando, alwalar tana karyewa ya ta6a da tafin hannun sane ko da cikin yatsun sa ko kuma da gefan hannu ko kuma da cindo (Dan yatsan da yake futowa amma da sharadi idan yana motsi) to alwalar sa ta karye. 


Haka zalika shafar mace ko mace ta shafi jikin namiji shima yana karya alwala, sai dai amma itama shafar ta rabu izuwa kaso hudu :

- Wanda yake da alwala ya ta6a mace ko kika ta6a namiji da niyar kiji dadi kuma kikaji da'din to alwala ta karye. 

- Wanda yake da alwala ya ta6a mace ko kika ta6a namiji ba da niyar kiji da'di ba kuma kika ji dadi alwala ta karye. 

- Wanda yake da alwala ya ta6a mace ko kika ta6a namiji da niyar kiji da'di bakiji dadi ba alwala ta karye. 

- Wanda yake da alwala ya ta6a mace ko kika ta6a namiji ba da niyar kiji da'di ba kuma bakiji da'din ba alwala tana nan bata karye ba. 

Amma alwala bata karyewa da shafar dubura, ko 'ya'yan maraina, ko amai ko cin naman tsohon raqumi, ko qaho da akewa mutum a cire masa mataccen jini shima baya karya alwala, ko kyakyata dariya a cikin sallah baya karya alwala amma sallar ta lalace, ko mace ta shafi al'aurarta baya karya alwala. 

A wani fadin akace amma idan ta saka 'dan yatsan ta a cikin al'aurar ta alwalar ta ta karye. 

الله ورسوله أعلم 

Allah ya kara fahimtar damu addini ya bamu ilimin da zamu bauta masa dashi saboda daidaiton Annabi a cikin sujjada lokacin da yake bautawa mahaliccin sa.


Article Translation in English Language.

The Maliki school of thought divides the things that break ablution into two groups: 

Hadasi and Sababan hadasi There are five hadiths, the three exits from the front of a person are: maziy, wadiy and bawali (urine). All these punishments are the same. 

If you have one ablution and it happens to you, then your ablution is broken and you have to perform another one. 

Then the Sababan hadasi are like: sleeping when you have ablution, sleep is also divided into four parts.

Long and heavy sleep, this sleep breaks ablution. 

- Short sleep which is not done for a long time but is also heavy, this sleep also breaks the ablution. 

- Sleep that is not long and light, this sleep does not break ablution. 

- A long, light sleep and it is time to perform ablution again, but the ablution is not broken. 

And the new ones who break the ablution are: 

when you have ablution, then you become crazy and your ablution breaks, or epilepsy, or you are drunk and you have ablution, you take intoxicants until they make you lose your mind and your ablution breaks. 

In the same way, ablution is broken by committing apostasy. If you have ablution and say something that will take you out of Islam (apostasy), then your ablution is broken, as well as doubt in hadith, for example, you doubt and urinate but you are not sure whether you are pure or not. 

It destroys ablution until you come up with what you doubt about it.

Ablution breaks if a person touches his front with his hand and there is nothing in between such as pants. 

condition if he is moving) then his awl is broken. In the same way, touching a woman or a woman touching a man's body also breaks ablution, but the touching is also divided into four parts: 

- A person who has ablution touches a woman or you touch a man with the intention of having fun and you do not enjoy it, then the ablution is broken. 

- A person who has ablution touches a woman or you touch a man without the intention of pleasure and you feel pleasure and the ablution is broken. 

- A person who has ablution touches a woman or you touch a man with the intention of having fun, but the ablution is not broken. 

- A person who has ablution touches a woman or you touch a man without the intention of getting pleasure and if you don't feel pleasure, the ablution is not broken. 

But ablution is not broken by touching the anus, or morning fruit, or vomiting or eating the meat of an old camel, or a horn used to remove dead blood from a person does not break ablution. 

Damaged, even if a woman touches her private parts does not break ablution. 

It is said that if she puts her finger in her genital area, her anus will break.

May God grant us more understanding about religion and bless us with the knowledge to worship Him because of the accuracy of the Prophet in prostration when he was worshiping his creator.

الله ورسوله أعلم 


SHARE THIS

Author:

Etiam at libero iaculis, mollis justo non, blandit augue. Vestibulum sit amet sodales est, a lacinia ex. Suspendisse vel enim sagittis, volutpat sem eget, condimentum sem.

0 comments: