Friday, November 22, 2024

Sallar kasaru kwana nawa ne?


Sallar kasaru kwana nawa ne

Adadin kwanakin yin kasaru uku 3 ne, ma'ana idan matafiyi yasan cewa bazaiyi kwanakin da suka wuce kwana uku ba, to kasaru ta hau Kansas matukar inda zaije yakai nisan mil arba'in da takwas.

Domin ita sallar kasaru tana badi ne akan matafiyin da yasan cewa inda za shi zaiyi kwanaki fiye da uku, ma'ana zaiyi kwana hudu Ko biyar Ko dai Sama da haka, saboda haka da zaran ya Isa masaukinsa Zai yi sallolinsa ne Kamar yadda ya Saba yi a gida. 

mazhabar malikiya idan matafiyi yabar gida da niyyar cewa ba zai wuce kwanaki uku ba zai dawo gida amma bayan da yaje sai bai samu daman kammala uzurinsa ba a cikin wannan kwanakin, to Zai cigaba da kasaru har zuwa lokacin da zai kammala abun da yaje yi matukar dai da niyyar cewa da zaran ya samu daman yin abin da ya kaishi Zai dawo Gina ne. Allahu A'alamu.



SHARE THIS

Author:

Etiam at libero iaculis, mollis justo non, blandit augue. Vestibulum sit amet sodales est, a lacinia ex. Suspendisse vel enim sagittis, volutpat sem eget, condimentum sem.

0 comments: