Zakka (zakka, zakka), daya ne daga cikin rukunan Musulunci guda biyar. Ma’ana zakka ta wajaba a kan musulmi, tare da sauran rukunan musulunci hudu
*Sallah
*Azumi
*Aikin hajji
*Imani da Allah da Manzonsa, Annabi Muhammad (SAW) (Kalmar shahadah).
Ga duk musulmi mai hankali, baligi, wanda ya mallaki dukiya akan wani adadi - wanda aka sani da Nisab - dole ne ya fitar da kashi 2.5% na wannan dukiyar a matsayin zakka.
Menene nisabin zakka?
Ana fitar da nisanin zakka ne akan darajar gram 87.48 na zinariya ko kuma giram 612.36 na azurfa.
Duk musulmin da dukiyarshi ta zarce darajar wadannan kudade dole ne ya fitar da zakkan Kashi 2.5% cikin dari na darajar dukiyarshi. Mutanen da ba su cika wannan ka'idar ba, ba zakka bata wajibta akan su ba.
Bari muyi kiyasin nisabin zakka a halin yanzu bisa la'akari da darajan zinare a Kasuwan Duniya da kuma darajan Naira akan Dalar amurka.
A yau Talata 30 July, 2024 ana sayar da gram 1 na zinare akan dalar Amurka $76.75 a kasuwar hada-hadar Zinare na www.goldprice.org
Kaga kenan zamu rubayya dala $76.75 na farashin zinare a halin yanzu da nisabin zakka na gram 87.48 na zinare.
$76.75 X 87.48= $6,714.09
Saboda haka Dalar Amurka $6,714.09 shine yawan kudin nisabin zakka a halin yanzu.
Don haka idan zamu chanja kudin daga Dalar Amurka zuwa Naira.
Farashin Naira akan Dalar Amurka $1 a yau shine Naira N1,660
Saboda haka nisabin zakka a naira shine $67.14.09 X N1,660 = N11,145,389.4 shine nisabin zakka a yau Talata 30 July, 2024.
Article Translation in English Language.
Zakka (Zakka, zakka), is one of the five pillars of Islam.
This means that zakat is obligatory on Muslims, along with the other four pillars of Islam
*Prayer
*Fast
* Pilgrimage
*Belief in God and His Messenger, Prophet Muhammad (PBUH) (the word shahadah).
Every sane, mature Muslim who owns a certain amount of wealth - known as Nisab - must pay 2.5% of that wealth as Zakat.
What is the ratio of tithing? The amount of tithe is calculated on the value of 87.48 grams of gold or 612.36 grams of silver.
Every Muslim whose wealth exceeds the value of these funds must pay zakkat 2.5% of the value of his wealth. People who do not fulfill this rule, do not pay tithe on them.
Let's estimate the amount of zakat currently based on the value of gold in the world market and the value of Naira against the US dollar. Today, Tuesday, July 30, 2024, 1 gram of gold is sold for USD 76.75 in the gold market of www.goldprice.org.
Let's imagine that we will multiply $76.75 of the current price of gold by the amount of zakat of 87.48 grams of gold. $76.75 X 87.48 = $6,714.09
Therefore, US$6,714.09 is the current amount of zakat. So if we change the currency from US Dollar to Naira.
The exchange rate of Naira to US$1 today is N1,660 Therefore, the amount of zakat in naira is $67.14.09 X N1,660 = N11,145,389.4 which is the amount of zakat today, Tuesday 30 July, 2024.
0 comments: