Biyayya ga iyaye wajibi ne a Musulunci kamar yadda Allah (S.W.T) yayi umurnin bin iyaye a ayoyin Alkur'ani da dama da hadisan Manzon Allah (S.A.W).
A cikin wannan mukalan zamu kawo maku yadda 'ya'ya yakamata su yi biyayya ga mahaifansa domin samun tsira a nan duniya da kuma gobe kiyama.
Saboda girman biyayyane zaka ga Allah (S.W.T) yana umurtan bayinsa muminai su yi biyayya ga iyayensu a duk lokacin da ya umurci a bauta mashi shi kadai.
A wani Hadisi,
Ibn Umar yace da Daisalata dan Mayyas: Kana so a rabaka da wuta kuma a shigar da kai AlJannah? sai nace eh Wallahi! Sai Ibn Umar yace: Iyayenka suna raye? sai nace mahaifiyata ce kawai, sai yace: Wallahi da zaka tausasa mata magana, kuma ka ciyar da ita abinci to da sai ka shiga Aljannah matukar baka yin manyan zunubai.
ﻋﻦ ﻫﺸﺎﻡ ﺑﻦ ﻋﺮﻭﺓ، ﻋﻦ ﺃﺑﻴﻪ ﻗﺎﻝ{ :ﻭﺍﺧﻔﺾ ﻟﻬﻤﺎ ﺟﻨﺎﺡ ﺍﻟﺬﻝ ﻣﻦ ﺍﻟﺮﺣﻤﺔ}، ﻗﺎﻝ: ﻻ ﺗﻤﺘﻨﻊ ﻣﻦ ﺷﻲﺀ ﺃﺣﺒﺎﻩ .
Daga Hisham dan Urwata daga Babansa yace: Game da ayar qur‘ani "Ka saukar musu da Fika-fikanka na tausayi" (wato su iyaye)
Hisham yace: Kada ka hana su wane abu idan suna sonsa. [Hadisan suna cikin Adabul-Mufrad].
Duk wanda yake sabama Iyayensa, yake sanya su bakin ciki, kuma baya tausaya musu to ya kiyaye makomar sa, duk wanda yake wulakanta iyayensa yake 'kin kula dasu to ba zai gama da duniya lafiya ba mutukar bai gyara ba.
Haka zalika duk wanda baya shirka da Allah, kuma baya aikata Manya Manyan Zunubai to zai Shiga Aljannah mutukar yana biyayya ga Iyayensa kamar yadda Ibn Umar yace.
Article Translation in English Language.
Obedience to parents is compulsory in Islam as Allah (S.W.T) commanded to obey parents in several verses of the Qur'an and the hadith of the Messenger of God (S.A.W).
In this article, we will tell you how children should obey their parents in order to be safe in this world and in the hereafter.
Because of the greatness of obedience, you will see Allah (S.W.T) commanding His believing servants to obey their parents whenever He commands to worship Him alone.
In another Hadith, Ibn Umar said to Daisalata son of Mayyas: Do you want to escape from hell fire and enter Jannah? I said yes by God Grace! Then Ibn Umar said: Are your parents alive? I said that she is only my mother, and he said: By God, if you speak softly to her, and feed her, then you will enter Paradise as long as you do not commit major sins.
In the Hadith of the authority of Hisham, son of Urwata, on the authority of his father, who said: Regarding the verse of the Qur'an, "Send down upon them Your wings of mercy" (that is, they are parents). Hisham said:
Do not deny them anything if they want it. [The hadiths are in Adabul-Mufrad].
Whoever disobeys his parents, makes them sad, and does not sympathize with them, he should protect his future, whoever insults his parents and refuses to take care of them, he will not end the world in peace unless he makes amends.
In the same way, whoever does not associate with God, and does not commit major sins, he will enter Paradise when he dies and obeys his parents, as Ibn Umar said.
0 comments: