Addu'a domin neman biyan bukatuwa cikin gaggawa, da yawan Al'umma na kokarin ganin samun biyan bukata nan take ga duk bukatun da suka roki Allah madaukakin sarki.
Hakikanin gaskiya shine Addu'a tana da matukar tasiri a cikin rayuwar musulmi amma kada mutum ya Zama cewa duk abin da ya roki Allah a nan Duniya shikenan Allah Zai biya masa, a'a ba haka abun yake ba, domin Allah madaukakin sarki Yana amsa Addu'ar duk wanda ya roke Shi da kyakkyawar niyya da kuma zuciya tsarkakakkiya Sai dai biyan bukatar Sai lokacin da Allah yaso ya Isa wannan Bawan nasa.
Zai Iya yuwuwa kayi Addu'ar samun yalwar arziki amma Allah (S.W.T) ya duba hakan a matsayin halaka a gare ka idan ya Baka a wannan lokacin don haka Sai ya jinkirta Maka zuwa Wani lokacin Ko kuma ma idan Yaga Dama ya sauya Maka ita da wata bukatar wacce ta fita alfanu a wajen Allah (S.W.T).
Haka Allah yake tafiyar da Al'amuransa ga bayinsa wadanda yake nufinsa da rahamarsa.
Don haka 'yan uwa mu riki Salatin Annabi (S.A.W) Shi kadai Kawai cikin ladani da ganin girman SHI wallahi Zai zame mana mafita GA duk kowace kalar damuwa da muke fama da dashi.
Article Translation in English Language.
Praying for urgent needs to be met, the majority of the community is trying to get immediate needs for all the needs that they have asked God Almighty.
The truth is that prayer is very effective in the life of a Muslim, but a person should not think that whatever he asks God for in this world, God will pay him, no, this is not the case, because God Almighty answers the prayer of everyone who asks Him with a good intention and a pure heart, except to fulfill the request.
When God wants, He will reach this servant of His.
It is possible for you to pray for abundance of wealth, but Allah (S.W.T) will see it as destruction for you if He gives it to you at this time, so He will delay it for you to another time or even if He sees the opportunity, He will change it for you.
A request that is beneficial to God (S.W.T).
This is how God manages His affairs for His servants who are His will and mercy.
Therefore, brothers and sisters, let's accept and manage to do the Salawat of Allah's Prophet (S.A.W) always only in the reward of seeing the greatness of HIM.
By God, He will be the solution to all the problems we are dealing with.
0 comments: