Wednesday, November 27, 2024

Adadin ayoyin alqur'ani nawane?

 Adadin ayoyin alqur'ani nawane?


Adadin Ayoyin dake cikin Alkur'ani mai girma 6236 ne banda Bismillah, idan kuma da Bismillah ne zasu zama 6,348. Saboda akwai Malaman mazhaban dake ganin cewa Basmalah bata a cikin Ayoyin Alkur'ani yayin da wasu ke kan fahimtar cewa tana cikin Ayoyin Alkur'ani mai girma.

Shi dai Alkur'ani mai girma an saukar da shine ga Annabi Muhammad (S.A.W) aya bayan aya a lokacin rayuwarsa tun daga lokacin da aka fara saukar da shi a gare sa da ayar "Iqra bi'ismi rabbikal ladhi khalaq" na suratul "Alaq".

Suratul Alaq itace surar farko da aka fara saukarwa ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W).

Article Translation in English Lang

The number of verses in the Holy Qur'an is 6236 without Bismillah, and if Bismillah were included it would be 6,348. 
Because there are scholars who believe that Basmalah is not in the verses of the Qur'an while others understand that it is in the verses of the great Qur'an. 

The Holy Qur'an was revealed to the Prophet Muhammad (S.A.W) verse by verse during his lifetime from the time it was first revealed to him with the verse "Iqra bi'ismi rabbikal ladhi khalaq" of suratul "Alaq". Suratul Alaq is the first chapter that was first revealed to the best creation, Prophet Muhammad (S.A.W).


ٱقْرَأْ بِٱسْمِ رَبِّكَ ٱلَّذِى خَلَقَ.

Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta.

خَلَقَ ٱلْإِنسَـٰنَ مِنْ عَلَقٍ.

Ya halitta mutum daga wani abu mai ɗaure.

ٱقْرَأْ وَرَبُّكَ ٱلْأَكْرَمُ.

Ka yi karatu, kuma Ubangijinka ne Mafi karimci

ٱلَّذِى عَلَّمَ بِٱلْقَلَمِ.

 Wanda ya koyar da alkalami.

عَلَّمَ ٱلْإِنسَـٰنَ مَا لَمْ يَعْلَمْ.

Ya sanar da mutum abin da bai sani ba.



SHARE THIS

Author:

Etiam at libero iaculis, mollis justo non, blandit augue. Vestibulum sit amet sodales est, a lacinia ex. Suspendisse vel enim sagittis, volutpat sem eget, condimentum sem.

0 comments: