Friday, September 29, 2023

Shika Shikan musulunci guda nawa ne?

 Shika Shikan musulunci guda nawa ne?

Shika Shikan musulunci guda nawa ne?

Amsa.

Shika Shikan musulunci guda biyar ne .

1. Kalmar Shahada

2. Sallah 

3. Azumi

4. Hajji

5. Zakka.

Shika Shikan musulunci guda biyar ne Kamar yadda yadda yazo cikin hadisin Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi, wadannan shika Shikan wajibi ne ga duk musulmin baligi kuma mai hankali Suna haɓaka ɗabi'a, suna ƙarfafa Musulunci ta hanyar haɗa kan musulmi kuma suna tunatarwa ga koyarwar Musulunci. Allah (S.W.T) ya umurci musulmi da su aiwatar da wadannan ayyuka kuma su yi koyi da Annabi Muhammad (S.A.W). Kowane ginshiƙi yana da nasa mahimmanci na musamman. 

1.KALMAR SHAHADA:
Kalmar Shahada shine shaidawa Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah (S.W.T) kuma Annabi MUHAMMAD (S.A.W) manzonsa ne kuma bawansa.

Kalmar Shahada kalma ce dake shigo da mutum cikin Musulunci, kuma dole ne a fade ta da tsarkin zuciya da yakini, 

اشْهَدُ انْ لّآ اِلهَ اِلَّا اللّهُ وَحْدَه لَا شَرِيْكَ لَه، وَ اَشْهَدُ اَنَّ مُحَمَّدً اعَبْدُهوَرَسُولُه

Fassarar ta a Hausa shine: " Na Shaida Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Muhammadu manzonsa ne". Kalma ce ta imani mai shaida kadaita Allah da cewa Muhammadu manzon Allah ne. Wannan kuma yana nuni da cewa dukkan annabawan da suka gabata manzanni ne kawai. 

Allah (S.W.T) ya ambaci Kalmar SHAHADA a cikin Alkur'ani mai girma a cikin suratul Ali-Imran ayata 18.

“Allah Ya shaida cewa, babu abin bautawa da gaskiya sai Shi, da mala’iku da ma’abuta ilimi – (Allah) Ya shaida (halitta) da adalci. Babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai hikima.”

2. SALLAH

Sallolin farilla guda biyar wajibi ga musulmi baligi mai hankali, itace ake kira da ibada mafi girma cikin ibadun da musulmai ke yi saboda girman sallah ba,a yarda aki yinta ba koda mutum yana cikin rashin lafiya ne matukar yana haiyacinsa sai ya gabatar da ita ko a cikin tunaninsa ne.

Sallolin farilla biyar wajibi ne ga dukkan musulmin. Yin Sallah ya kunshi motsin jiki kamar sujada ga Allah, Ruku'u karatun ayoyin Alqur'ani zaman Tahiya da yin Salati ga Annabi MUHAMMADU (S.A.W). Sallah hanya ce ta sadarwa da godiya da ambaton Allah (S.W.T). 

Sallolin farilla biyar sune

1. Sallah Asubahi

2. Sallar Azuhur

3. Sallar La'asar

4. Sallar Magriba

5. Sallar Isha'i

3. AZUMI

Article Translation in English Language.

There are five pillars of Islam. 

1. The Word of Shahada 

2. Prayer 

3. Fasting 

4. Hajj 

5. Zakkat. 


There are five pillars of Islam. 

As mentioned in the hadith of the Messenger of God, may God's peace and blessings be upon him, these pillars are obligatory for all mature and intelligent Muslims. 

They promote morality and strengthen Islam by uniting Muslims and they remind the teachings of Islam. Allah (S.W.T) ordered Muslims to carry out these actions and follow the example of Prophet Muhammad (S.A.W). 

Each column has its own special significance.

1. KALIMATU SHAHADA: 

The word Shahada means testifying that there is no god but Allah (S.W.T) and Prophet MUHAMMAD (S.A.W) is his messenger and servant. 

The word Shahada is a word that brings a person into Islam, and it must be said with purity of heart and conviction.

2. PRAYER 

The five mandatory prayers are obligatory for a mature Muslim, it is called the greatest act of worship among Muslims because of the greatness of the prayer, it is permissible to perform it even if a person is sick, as long as he is pregnant, he should perform it or it is in his mind. 

The five obligatory prayers are obligatory for all Muslims. Praying consists of physical movements such as prostration to God, bowing, reciting verses of the Qur'an, sitting in Tahiya and praying to the Prophet MUHAMMAD (S.A.W). 

Salah is a way of communicating, thanking and mentioning Allah (S.W.T). 

The five obligatory prayers are: 

1. Fajr Prayer (Dawn prayer)

2. Dhuhr prayer (early afternoon prayer)

3. Asr Prayer (late afternoon prayer)

4. Maghrib prayer (sunset prayer)

5. Isha'a prayer  (night prayer).



SHARE THIS

Author:

Etiam at libero iaculis, mollis justo non, blandit augue. Vestibulum sit amet sodales est, a lacinia ex. Suspendisse vel enim sagittis, volutpat sem eget, condimentum sem.

0 comments: