Wednesday, March 1, 2023

Menene Musulunci?

 


Assalamu Alaikum warahmatullahi ta'ala Wabarakatuhu.

Yan uwa musulmi bayan gaisuwa irin ta addinin Musulunci, muna maku fatan Alkairi da fatan kuna Cikin koshin lafiya.

A yau inshaAllah zamu tattauna ne akan Menene ma'anar Musulunci, ma'ana me ake nufi da zaran kaji an ambaci kalmar Musulunci.
Kamar yadda yazo a cikin Alqur'ani Mai Girma da hadisan ma'aiki sallallahu alaihi wasallam.
Musulunci Addini ne Wanda a halin yanzu yake da kimanin mabiya biliyan daya da miliya dubu dari takwas (1.8 Billion) wato kimanin kaso 24% Cikin dari na Al'ummar duniya Musulmai ne.

Wadannan kasashen guda goma sune kan gaba a jerin kasashen dake da yawan Musulmai a fadin duniya.

1. Indonesia (231,000,000)
2. Pakistan (212,300,000)
3. India (200,000,000)
4. Bangladesh (153,700,000)
5. Nigeria (95,000,000–103,000,000)
6. Egypt (85,000,000–90,000,000)
7. Iran (82,500,000)
8. Turkey (74,432,725)
9. Algeria (41,240,913)
10. Sudan (39,585,777).


Musulunci kalma ce ta Larabci wacce ke nufin sallamawa da mika wuya gaba daya ga Allah madaukakin Sarki, Mahaliccin kowa da komai.

Musulunci addini ne na tauhidi da yake karantar da cewa babu abin bautawa da gaskiya Sai Allah, mahaliccin duniya da duk abin dake cikinta. 

Mu Musulmai munyi imani cewa Musulunci shine addinin gaskiya na Allah da aka saukar ga dan Adam.
Musulunci cikakkiyar hanya ce ta rayuwa wacce ta shafi kowane bangare na rayuwa. 

Musulunci bai bar wata kafa ba kamar yadda yake karantar da dan Adam kan yadda ya kamata ya tafiyar da kowane fanni na rayuwarsa kamar zamantakewa da kyawawan halaye da da'a da shari'a da al'adu da siyasa da tattalin arziki.

Ma'anar Musulunci shine: Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya Sai Allah, kuma Annabi MUHAMMADU (S.A.W) manzon Allah ne, sai tsayar da Sallah da bayar da Zakka da azumtar watan Ramadan da kuma zuwa aikin Hajji ga wanda ya samu iko. Kamar dai yadda yazo a cikin Hadisin Manzon Allah (S.W.A)




Wadannan Sune shika-shikan Musulunci guda biyar wadanda suka wajjaba kan kowane Musulmi baligi.

Wanene Musulmi?
Musulmi shine Wanda ya sallama har Cikin zuciyarsa cewa babu abin bautawa da gaskiya Sai Allah Kuma Annabi MUHAMMADU bawan sa ne kuma Manzonsa,
لآ اِلَهَ اِلّا اللّهُ مُحَمَّدٌ رَسُوُل اللّهِ
"La ilaha illa Allah. Muhammad rasool Allah"
Duk wanda ya furta wannan kalmar to shi Musulmi ne kamar dai yadda ya zo acikin Hadisin Manzon Allah (S.A.W)

Article Translation in English Language.

Assalamu Alaikum warahmatullahi taala Wabarakatuhu. Dear Muslim brothers and sisters, after the greetings of the Islamic religion, we wish you Al-Kairi and hope that you are in good health. 


Today, God willing, we will discuss the meaning of Islam, meaning what is meant when the word Islam is mentioned. As mentioned in the Holy Qur'an and the hadith of the Prophet, peace and blessings be upon him. 


Islam is a religion that currently has about one billion and eight hundred million (1.8 billion) followers, that is about 24% of the world's population are Muslims. 

Islam is an Arabic word that means submission and complete surrender to God Almighty, the Creator of everything and everyone.

Islam is a monotheistic religion that teaches that there is no true deity except Allah, the creator of the world and everything in it. We Muslims believe that Islam is the true religion of God revealed to mankind. Islam is a complete way of life that covers every aspect of life. 

Islam has left no stone unturned as it teaches mankind how to manage every aspect of his life such as social, moral, moral, legal, cultural, political and economic. 

The meaning of Islam is: Testifying that there is no god but Allah, and the Prophet MUHAMMAD (S.A.W) is the Messenger of God, except to establish Salah, give Zakat, fast the month of Ramadan and go to Hajj for the one who has the power. As mentioned in the Hadith of the Messenger of God (S.W.A)

These are the five pillars of Islam that are obligatory on every adult Muslim. 

Shahadah: The Muslim profession of faith, which states "There is no God but God (Allah), and Muhammad is His Messenger" 

Salah: The performance of ritual prayers five times a day 

Zakat: The act of giving a portion of one's income to those in need 

Fasting: Fasting during the month of Ramadan 

Hajj: The pilgrimage to the holy city of Mecca 

Who is a Muslim? A Muslim is one who submits in his heart that there is no true deity but Allah and the Prophet MUHAMMAD is his servant and his Messenger. 

For Allah "La ilaha illa Allah. Muhammad Rasool Allah" Anyone who utters this word is a Muslim as it is in the Hadith of the Messenger of God (S.A.W).


SHARE THIS

Author:

Etiam at libero iaculis, mollis justo non, blandit augue. Vestibulum sit amet sodales est, a lacinia ex. Suspendisse vel enim sagittis, volutpat sem eget, condimentum sem.

0 comments: