ALLAH MAI GAFARA NE
KASHI NA DAYA (01)
Godiya tare da yabo sun tabbata ga Allah mai rahama mai jinkai.
Wanda yace: “KACE YAKU BAYINA WADANDA SUKA YI MUNANAN AYYUKA, KADA KU YANKE KAUNA DAGA RAHAMAR UBANGIJI. HAKIKA LALLAI ALLAH YANA GAFARTA ZUNUBAI BAKI DAYA, DOMIN SHI MAI GAFARA NE, MAI KUMA JINKAI NE.”
Tsira da Amincin Allah sun tabbata ga Annabin rahama, wanda Allah (S.W.T) ya aiko shi rahama ga talikai, tare da Alayensa da Sahabbansa.
Bayan haka: Shiga tsakanin Allah (S.W.T) Mahalicci da abin halittansa akwai hatsari matuka. Domin matukar bawa ya furta kalmar shahada, ya kuma halasta halas, ya haramta haram, to ya kubuta daga hannun kowanne mutum ko Kungiya, duk laifin da ya aikata lamarinsa yana wajen Allah.
Imam Ahmad ya ruwaito wani hadisi. Wani mutum yazo wajen manzon Allah (S.A.W) (TSOHO NE MATUKA YANA DOGARE DA SANDA) yace: ya manzon Allah lallai na aikata miyagun ayyuka da fajirce-fajirce, shin za’a gafarta Mani, san manzon Allah (S.A.W) yace: SHIN BAKA SHAIDA ALLAH DAYA BANE? SAI TSOHON YACE: NA SHAIDA KUMA NA SHAIDA KAI MANZON ALLAH NE. SAI MANZON ALLAH (S.A.W) YACE : HAKIKA AN GAFARTA MAKA MIYAGUN LAIFUFFUKANKA DA FAJIRCE-FAJIRCENKA.
Kuma ku dubi Hadisin da ABU SA”IDUL KUDRI (R.A) ya ruwaito daga manzon Allah (S.A.W) Kamar yadda yazo a cikin Bukhari da Muslim, inda wani mutum ya kashe mutane casa’in da tara (99) sai yayi nadama ya zo ya tambayi wani mai bauta daga Cikin bani isra’ila, shin ko akwai hanyan tuba?
Sai yace masa a’a hanyan tuba. Wato kunga ya Shiga tsakaninsa da Mahaliccinsa kenan, har ya san Allah ba zai gafarta masa ba. Sai mai laifin nan yace: to tunda babu hanyar tuba to bari in cika darin da kai, sai ya kashe shi.
Daga nan sai ya tambayi wani malami daga Cikinsu, shin akwai kofar tuba? Sai malamin yace: WA YA ISA YA SHIGA TSAKANIN BAWA DA MAHALICCINSA YA HANA SHI TUBA?
Sai malamin yace akwai hanyan tuba, sai malamin ya umurceshi daya bar garin da yayi laifuffukan, ya koma Garin da ake bautan Allah (S.W.T).
Sai ko ya nufi garin, akan hanyarsa mala’ikan mutuwa ya iske shi. Sai mala’ikun rahama da na azaba suka fara jayayya wannan na cewa, shi zai karbi ransa wannan na cewa shi zai karba. Nan take Allah (S.W.T) ya umurcesu da su aina inda ya fito da inda zashi aga inda yafi kusa, sai akaga yafi kusa daga inda zaiyi HIJIRA da takawa daya tak. Sai mala’ikun rahama suka amsa abin su.
Ance Allah ne (S.W.T) ya umurci Garin alherin da ta kusance shi ya kuma umurci garin banzan da ta nisanceshi saboda tsananin rahamar Ubangiji.
Saboda haka duk mai hankali ba zai Shiga tsakanin bawa da Mahaliccinsa ba, domin mutum sirrin Allah ne, kai dai GA MUTUM.
Don haka ne mu bama kafirta mai kalmar shahada duk laifuffukansa, kamar yadda manzon Allah (S.A.W) yace: KUYI SALLAH A BAYAN WANDA YACE LAILAHA ILLALLAHU kuma Kuyi ma wanda yace LAILAHA ILLALLAHU SALLAH IDAN YA MUTU.
Jama’ar Musulmi mu daina iyakance falalar Allah da rahamarsa domin yin hakan laifi ne babba……..a dakace mu ,zamu cigaba.
Article Translation in English Language.
Thanks and praise be to God, the Merciful, the Merciful. Wanda said: "TELL ME THOSE WHO HAVE DONE EVIL DEEDS, DON'T DROP YOUR LOVE FROM THE LORD'S MERCY." GOD FORGIVES ALL SINS, BECAUSE HE IS FORGIVING AND MERCIFUL."
Peace and Peace of God are guaranteed to the Prophet of mercy, whom God (S.W.T) sent as a mercy to the worlds, along with his Companions and Companions.
After that: Interference between God (S.W.T) the Creator and His creation is extremely dangerous.
Because as long as a servant utters the word martyrdom, and makes lawful and prohibits haram, then he escapes from the hand of any person or group, all the crime he committed in his case is with God.
Imam Ahmad narrated a hadith.
A man came to the Messenger of God (S.A.W) (THE OLD DEAD DEPENDS ON A STICK) and said: O Messenger of God, I have indeed committed bad deeds and acts of immorality.
Will you forgive me? The Messenger of God (S.A.W) said: HAVE YOU EVIDENCE GOD IS ONE? THEN THE OLD MAN SAID: I WITNESS AND I WITNESS THAT YOU ARE THE MESSENGER OF GOD. THE MESSENGER OF ALLAH (S.A.W) SAID:
INDEED YOU HAVE BEEN FORGIVED OF YOUR EVIL CRIMES AND FAJIR-FAJIR. And look at the Hadith narrated by ABU SAIDUL KUDRI (R.A) from the Messenger of God (S.A.W).
Ask a worshiper from among the people of Israel, is there a way to repent? Then he told him no to the way of repentance. In other words, he came between himself and his Creator, until he knew that God would not forgive him.
Then the criminal said: since there is no way to repent, let me fill the hundred with your head, so he killed him.
Then he asked a teacher from among them, is there a door to repentance? Then the teacher said: WHO IS ENOUGH TO COME BETWEEN A SERVANT AND HIS CREATOR FORBIDDEN HIM TO REPENT?
Then the teacher said that there is a way to repent, so the teacher ordered him to leave the city where he committed the crimes, and return to the city where God (S.W.T) is worshipped.
Even though he was going to the town, on his way the angel of death took his life.
Then the angels of mercy and the angels of punishment started arguing, this one saying, he will take his life, this one saying he will take it.
At that moment Allah (S.W.T) ordered them to go from where he came from and where he was going to and where he was going to, and it was seen that it was the closest from where he would migrate with one step.
Then the angels of mercy answered their question. It is said that God (S.W.T) ordered the city of grace to approach him and ordered the city of vanity to stay away from him because of God's great mercy.
Therefore, every intelligent person will not come between a servant and his Creator, because man is God's secret, it is for man.
That's why we don't disbelieve the one who says martyrdom for all his crimes, as the Messenger of God (S.A.W) said: PRAY BEHIND THE ONE WHO SAID LAILAHA ILLALLAHU AND PRAY FOR THE ONE WHO SAID LAILAHA ILLALLAHU SALLAH WHEN HE DIED.
My Dear Muslim brothers, we should stop limiting God's grace and mercy because doing so is a big crime...
0 comments: